Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Saudiya ta zartar wa mutane biyar hukuncin kisa bisa aikata laifin ta'addanci

  Saudiyya ta zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane 5, hukuncin da ke zama irin sa mafi girma a bana, bayan samun su da laifin kaddamar da...

 


Saudiyya ta zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane 5, hukuncin da ke zama irin sa mafi girma a bana, bayan samun su da laifin kaddamar da harin ta’addanci a masallatan kasar.

Mutanen biyar da suka hadar da 'yan asalin Saudiyyan 4 da kuma dan asalin kasar Masar daya sun amsa laifin kaddamar da harin ta‘addancin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata da dama a gabashin kasar mafi arzikin man fetur.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa, mahukuntan Saudiyya basu bayyana lokacin da mutanen suka kai hare-haren ko kuma masallatan da suka kaiwa harin ba.

Kawo yanzu dai babu karin haske game da hanyar da aka bi wajen zartaswa da mutanen hukuncin kisan, sai dai kuma abu ne sananne yadda kasar ke zartas da irin wannan hukuncin ta hanyar rataya ko kuma fille kai. See less



No comments