Daga Abubakar M. Taheer Da yammacin ranar Juma'a Dandalin daliban Harkar musulunci dake karatu a jami'ar Kimiyya da Fasa...
Daga Abubakar M. Taheer
Da yammacin ranar Juma'a Dandalin daliban Harkar musulunci dake karatu a jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil (ADUSTECH) sun gabatar da gagarumin taron Ghadir.
Taro da aka fara da budewa da addu'a daga bakin Hussaini A Tsoho sai jawabin Maraba daga bakin Yusura Nalado.
Daga nan aka gabatar da Malam Auwal Iliyasu domin gabatar da jawabi.
Cikin jawabin nasa Malamin ya yi dogon bayani kan darajoji da karamomin Imamu Ali wanda hakan ke da alaƙa da kusancinsa da Allah maɗaukakin sarki a cewarsa.
Malamin ya kara da cewa Imamu ya cancanci zama wasiyya Manzo Allah ta dukkan ma'anoni wanda Allah ya bama Manzonsa umarni na nasaba shi a matsayin wasiyyalinsa domin sakon Annabta ya zama ya kammala.
Da take na ta jawabi Malama Fatima Tafida ta kawo irin maganganun malamai daga bangarori daban-daban wanda suka kawo tarihin ranar Ghadir wanda hakan ya nuna ranar Ghadir ba baƙuwa bace ga dukkan bangarorin addinin Musulunci.
Haka kuma ta kara da umarnin da Manzon Allah (SAWW) ya bada na cewa wanda ya ji ya isar da wanda bai jima sakon nasabcin Imamu Ali.
Daga karshe aka saka Jawabin Jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibraheem Zakzaky na Ghadir wanda ya gabatar na wannan shekarar a matsayin jawabin rufewa.
Bayan Kammala a gabatar da walima ta murna da wannan rana tare da daukan hotuna domin sada zumunci.
No comments