Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo ya yi ta'aziyyar rasuwar matar Tafida Sarkin Samarin Agege

Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Farfesa Ad...


Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Tafidan Sarkin Samarin Agege, Alhaji Ibrahim Iro Garba bisa rasuwar matarsa, Saiyyada Hafsa Saiyadi Usman Bashir. 

Marigayiya Saiyyada Hafsa mai shekaru 40, ta rasu ne a ranar Alhamis 5 ga Yuli 2023 a gidan aurenta a Kano bayan gajeruwar rashin lafiya. 

A sakon ta'aziyyar da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi, Farfesa Gwarzo ya bayyana matukar kaduwarsa bisa rasuwar Saiyyada Hafsat. 

Ya bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ba kawai ga mijinta ba da iyalanta ba harma ga iyayenta da kuma 'yan'uwa da abokan arziki. 

Farfesa Gwarzo har wala yau ya jajantawa iyalai da mijin marigayiyar wanda yake rike da sarautar gargajiya ta Tafidan Sarkin Samarin Agege da kuma Dan Adalan Turai bisa rasuwar Saiyyada Hafsat wanda ya bayyanata a matsayin mata mai kirki da biyayya. 

"a madadin iyalina, hukumar gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ina mika sakon ta'aziyyarmu zuwa gareka da iyalin marigayiyar bisa wannan babbar rashi,", in ji Farfesa Gwarzo. 

Ya kuma yi addu'ar Allah ta'ala ya bai wa dukkanin iyalai hakuri da juriyar wannan babbar rashi da aka yi wanda ba za a iya mayarwa ba.   

Farfesa Gwarzo wanda tuni ya tashi ya yi takanas ya kai wa mijin marigayiyar ziyarar ta'aziyyah a gidansa dake Gwammaja hedikwatas dake cikin kwaryar Kano, ya yi addu'ar Allah ya jikanta da Rahama, ya kuma gafarta mata kurakuranta ya kuma ba ta ladan kyakkyawan ayyukanta da Aljannah Firdaus. 

Marigayiyar ta rasu ta bar 'ya'ya maza biyu kuma tuni aka bizne ta a Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. 

Allah ya jikanta da Rahama. Ameen.

No comments