Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatin kasar na bai wa gidajen talakawan Nijeriya miliyan 12 Naira 8,000 na tsawon watanni sh...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatin kasar na bai wa gidajen talakawan Nijeriya miliyan 12 Naira 8,000 na tsawon watanni shida.
Hakan na kunshe cikin wata wasika da shugaban kasar ya rubuta wa majalisar wakilai dangane da bukatar gwamnatin Buhari ta karbo bashin dala miliyan 800 domin shirin rage raÉ—aÉ—in talauci
Shugaban kasar na neman amincewar majalisar ne domin samun bashin.
Don tabbatar da kudin sun isa ga talakawan, Shugaban ya ce za a tura kudin zuwa asusun aiyarsu ta banki.
A bangare guda, majalisar wakilan Najeriya ta amince da naira biliyan 500 a matsayin kuƙin rage raɗaɗin cire tallafin mai fetur.
Majalisar ta amince da kudin ne bayan nazari da buƙatar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar na yin gyara a dokar karin kasafin kudin shekarar 2022.
Kakakin majalisar Rt. Hon. Abbas Tajudeen, PhD, ne ya karanta wasikar shugaban kasar a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ya shugaban kasar ya bukaci a gyara ga dokar da za a ware naira biliyan 500 ga shirin tallafa wa Æ´an Najeriya bayan raÉ—aÉ—in cire tallafin man da suka shiga.
Wasikar Shugaba Tinubun na cewa “Na rubuta wa Majalisar Wakilai wannan wasika domin neman amincewarta wajen yin gyara a dokar karin kasafin kuÉ—in 2022''.
“BuÆ™atar ta zama dole saboda a samu kuÉ—in da ake buÆ™ata don samar da abubuwan da zai rage wahalar cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.
“Duk da ina fatan majalisar wakilai za ta yi la’akari da wannan bukata cikin gaggawa, don Allah a yarda''.
A zaman majalisar na ranar Alhamis, wanda kakakin majalisar Tajuden Abbas ya jagoranta, ‘yan majalisar da dama da suka yi magana kan bukatar, sun bayyana goyon bayansu ga cire tallafin mai da kuma shirye-shiryen majalisar na mara wa gwamnatin Tinubu baya kan yadda za a shawo kan illolin da cire tallafin ya jawo wa Æ´an Najeriya.
No comments