Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mace ɗaya tilo da ke takarar shugaban ƙasa a Zimbabwe

  An sanya sunan Elisabeth Valerio, cikin jerin sunayen 'yan takarar shugaban kasar Zimbabwe a zaben da za a gudanar cikin watan Agusta ...

 


An sanya sunan Elisabeth Valerio, cikin jerin sunayen 'yan takarar shugaban kasar Zimbabwe a zaben da za a gudanar cikin watan Agusta mai zuwa, bayan da ta samu nasara a kotun daukaka kara kan hana ta shiga zaɓen .

Elisabeth Valerio ta yi nasarar kalubalantar matakin da hukumar zaɓen ƙasar Zimbabwe ta dauka na kin amincewa da takardun takararta.

Jami’an hukumar zaɓen kasar sun ce ta gaza biyan dala 20,000 kudin takardar shiga takarar.

To sai dai Misis Valerio ta ce ta sayi fom din, sannan ta aike wa hukumar da shaidar kudin sayen fom din.

Cikin karar da ta shigar a gaban kotun, Misis Valerio ta ce ta bayar da shaidar tura kuɗi ta banki.

A farkon wannan watan ne ta ce ana hana mata a Zimbabwe damar shiga siyasa.

Yanzu dai ‘yan takara 12 ne ke neman shugabancin kasar inda za a gudanar da zaben ranar 23 ga watan Agusta.

No comments