Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilan Da Yasa Kyari Ya Maye Gurbin Adamu A Matsayin Shugaban APC

Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara daya da 'yan watanni yana...

Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara daya da 'yan watanni yana jagorantar jam'iyyar.

Sabon shugaban riƙo na jam'iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus din Adamu kwana guda bayan kafafen yada labarai a Najeriya suka wallafa labarin cewa rashin jituwa tsakanin Sanata Adamu da shugaba Tinubu ya tursasa masa yar da ƙwallon mangwaro

Shugaban jam’iyyar ta APC ya bar mukamin ne kimanin wata biyar bayan ya jagorance ta a zaben shugaban kasar, inda ta yi nasara.

Bayanai sun ce Adamu ya ajiye aikin ne tare da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore.

Akwai dai alamu na cewa an dinga samun takun-saka a cikin jam’iyyar tun bayan da shugaba Tinubu ya kama mulki, kimanin watanni biyu da suka gabata.

Ajiye muÆ™amin shugaban jam’iyyar zai iya alamta cewa akwai wani babban rikici ne tsakanin Æ´aÆ´an jam'iyyar da aka kasa samun masllaha.

A lokacin da ya sanar da ajiye muÆ™amin na Abdullahi Adamu, shugaban riÆ™on jam’iyyar na Æ™asa, Abubakar Kyari ya ce Sanata Adamu bai bayyana dalilin ajiye muÆ™amin nasa ba.

Kwamitin gudanarwa na APC din a zamansa na ranar Litinin ne ya amince da naɗa Sanata Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar a ɓangare arewacin Najeriya a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar.

A watan Maris ɗin 2022 ne aka zaɓi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa bayan gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi shugaban riƙo na kusan shekaru biyu.

'Takun-saka da Tinubu'

A watan Yunin 2022, ana jajibarin zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da cewa sun yanke shawarar goyon bayan Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai riƙe tutar APC a zaɓen 2023 kuma shi ne zai kasance ɗan takarar maslaha.

Lamarin ya tayar da ƙura a tsakanin ƴan siyasa inda waɗansu da dama suka nuna cewa bayan shugabancin Buhari na shekara takwas ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya.

Daga bisani tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben fitar da gwanin kuma ya zama dan takarar APC a zaben da aka yi a farkon wannan shekarar.

Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a karshen watan Mayu.

Tun daga lokacin ne rahotanni ke cewa ana zaman doya da manja tsakanin Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu da kuma fadar shugaban kasa, kuma hakan bai rasa nasaba da abin da ya sa Adamun ya yar da ƙwallon mangwaro ya huta da kuda.

Ko a farkon wannan watan ma, Sanata Abdullahi Adamu ya yi ɓaɓatu game da cikon shugabannin da aka sanar na majalissun dokokin kasar, inda ya nuna rashin gamsuwa da zaɓen da aka yi na masu rinjaye da mai tsawatarwa da wadansu mukaman wadanda ya ce ba a tuntuɓe su ba kafin yanke shawara.

No comments