Gwamnan Jihar Katsina, Dauda Lawal ya ziyarci Katsina don yin ta'aziyya ga Shugaban Kamfanin Jirgin Max, Alhaji Dahiru Barau...
Gwamnan Jihar Katsina, Dauda Lawal ya ziyarci Katsina don yin ta'aziyya ga Shugaban Kamfanin Jirgin Max, Alhaji Dahiru Barau Mangal bisa rasuwar matarsa.
Shahararren É—an kasuwa, Mangal ya rasa matarsa Aisha ne a ranar asabar É—in da ta gabata a babban birnin tarayya, Abuja.
Gwamna Lawal a wata takardar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa wacce iyalanta za su yi kewar rashinta.
Haka nan kuma ya yi addu'ar Allah Ya yi wa marigayiyar sakamako da masauki a Aljannah.
"Mun zo ne domin yin jaje da ta'aziyya na wannan gagarumin rashi da aka yi. Muna jajantawa dukkanin iyalai da 'yan uwa.
"Wannan lokaci ne mai tsanani ga ilahirin iyalan marigayiyar da ma É—aukacin al’ummar Katsina. Allah Ya Æ™arfafeku da juriyar wannan rashi."
No comments