Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Saturday, June 14

Pages

Labarai:

Rundunar 'Yan sanda Ta Dakile Hari A Masallacin Juma'a Da Kashe ‘Yan Bindiga A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim Rundunar ‘Yan Sandan jihar Zamfara ta yi nasarar dakile wani shiri da wasu ‘yan bindiga suka shirya kai wa a Masallaci...


Daga Hussaini Ibrahim

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Zamfara ta yi nasarar dakile wani shiri da wasu ‘yan bindiga suka shirya kai wa a Masallacin Juma’a a kauyen Kwata da ke karkashin gundumar Magarya a karamar hukumar Zurmi a yau Juma’a.

Jami'in hulda da rundunar 'Yan Sandan na jihar Zamfara,(PPRO) ASP Yazid Abubakar ne ya bayyyana haka a taron manema labarai a Gusau.

PPRO, Yazid ya bayyyana cewa, Jami'an sun samu rahotan siri na Magarya na shirin kai hari wanda anan take suka dauki matakin gaggawa na dakile harin.

Ya kuma kara da  cewa, maharan sun kai kimanin mutane biyar dauke da makamai a kan babura biyu da ake zargin ‘Yan Bindiga ne da ke shirin kai  hari a lokacin sallar Juma’a a Kauyan Kwata da ke cikin Karamar hukumar Zurmi.

“Anan take Jami'an mu sukai artabu da 'yan bindigar wanda ya dauki tsawon sa’a guda ana yi, inda aka kashe daya daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu kuma suka tsere zuwa daji.sun gudu sunbar bindiga AK47 guda biyu, alburusai hudu na 7.62mm da kuma babur Bajaj.a ta akin Jami'in hulda da Jama'a na Rundudar.

Hakazalika, jami’an ‘Yan Sandan da ke aiki a Zurmi sun samu rahotan siri na cewa, wasu gungun ‘yan bindiga ne na shirin kai hari kan jami’an ‘yan sanda a karamar hukumar Zurmi.

A cewar PPRO, da samun labarin, DPO ya jagoranci tawagar da suka binciki lamarin wanda ya yi sanadin cafke wata Mata ‘yar shekara 35 mai suna Umma Zubairu da ke kauyen Rukudawa da ke Awala ta hanyar Nasarawan Zurmi kan harin da aka shirya kai wa ‘Yan Sanda a  Zurmi. .

“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa, tana aiki da dan fashin mai suna ‘Dan karami Gwaska’ a matsayina na  mai ba shi labarun siri kuma an tura ta ne ta sanya ido kan ‘yan sanda a Zurmi domin su kai hari, an bincikar wanda ake zargin kuma an gurfanar da ita a gaban kotu a yanzu Haka.

Kuma Rundudar ta kama shahararun masu fashin mashina da Suka addabi Jihar ta Zamfara.

No comments