Daga Ammar Muhammad Rajab A ranar Laraba 21 ga watan Fabrairun 2024 ne aka gudanar da gagarumin taro a Abuja domin yi wa Shaikh ...
Daga Ammar Muhammad Rajab
A ranar Laraba 21 ga watan Fabrairun 2024 ne aka gudanar da gagarumin taro a Abuja domin yi wa Shaikh Zakzaky gaisuwar dawowarsa daga ƙasar Iran. Dubban ɗaruruwan mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya ne suka cika titunan Abuja domin miƙa wa Shaikh Ibraheem Zakzaky mubaya'arsu.
Bayan tafiyar kwanaki 130 yana jinya a Iran, Shehin malamin da matarsa Malama Zeenah, sun dawo, bayan sun kammala jinyarsu wacce take da muhimmanci sakamakon raunukan da suka samu a kisan kiyashin da sojoji suka yi a Zariya a watan Disambar 2015.
Bayan da aka ɗauki tsawon lokaci mahukuntan Nijeriya a lokacin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na ci gaba da take haƙƙinsa wajen riƙe takardunsu na fita ƙasashen waje, Shaikh Zakzaky tare da mai ɗakinsa sun isa Iran domin duba lafiyarsu ne a ranar 14 ga watan Oktoban 2023.
Al'umma da dama ne suka cika filin wasa na Moshood Abiola Stadium dake birnin Tarayya Abuja da misalin Æ™arfe 7 na safiyar Laraba suna jiran isowar Jagoran Harkar Musuluncin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe wanda ya iso da misalin Æ™arfe 1:30 na rana. Daga filin jirgin saman inda wasu ‘yan'uwa da magoya bayansa suka tarbe shi, motocin malamin da suka Æ™unshi baÆ™ar mota Æ™irar SUV guda uku da wata mota Æ™irar Bas, kai tsaye suka zarce zuwa filin wasa na kasa.
A kofar birnin Abuja, da aka fi sani da Abuja City Gate, al'umma da dama ne suka taru, riÆ™e da tutoci da banoni, suna lale maraba da babban Shehin malamin da ya rasa ‘ya’yansa maza har guda uku da mabiya sama da 1000 a wani farmaki na kwanaki uku da sojojin Nijeriya suka kai masa a gidansa dake Gyallesu da makarantu da wuraren ibada a garin Zariya na jihar Kaduna a shekarar 2015.
A ranar Larabar ita ce karo na farko a tsawon shekaru biyu da rabi da sakin Shehin Malamin da wata babbar kotu ta yi a Kaduna da ya bayyana a taro mai yawan al'umma, inda ya haÉ—u da mabiyansa.
A lokacin da yake jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya nemi afuwar mahalarta taron bisa jinkirin da aka samu na isowar jirgin nasa, wanda tun da farko an shirya sauka da ƙarfe 7 na safe a Abuja. Ya kuma bayyana abubuwan da ya faru a lokacin ziyarar jinyar tare da miƙa godiyarsa ga mabiyansa bisa nuna jajircewa da sadaukarwa da suka yi a lokacin kisan kiyashin da aka yi a Zariya.
Jaridar MADOGARA har wala yau ta labarto cewa, a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Shehin Malamin da mai É—akinsa suka sauka a birnin Tehran, inda manyan baki da dama suka tarbe su.
Ziyarar Shehin Malamin da matarsa na zuwa ne bayan takun saƙa da hukumomin Nijeriya a ƙarƙashin Buhari da suka yi domin a ba su takardun tafiye-tafiyensu da aka riƙe musu tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Zariya a shekarar 2015. Wanda gwamnati mai ci ta Bola Ahmad Tinubu suka sakinsa musu takardunsu da ya ba su damar tafiya ƙasar waje domin neman lafiyarsu.
Bayan isar sa babban birnin ƙasar Iran, Shaikh Zakzaky ya samu ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, kafin daga bisani suka wuce birnin Mashhad domin neman lafiya.
A yayin zaman jinyarsu, Jami'ar Tehran ta ba Shaikh Zakzaky digirin girmamawa kuma ya samu yabo da jinjina daga cibiyoyin malamai na Ƙum da Mashhad.
Bugu da ƙari, ya halarci wani taron wayar da kan al'umma a kan lamarin Falasɗinu na ƙasa da ƙasa, wanda ya samu halartar malaman addinin Musulunci daga ƙasashe da mazhabobi, ciki har da Sheikh Ahmad Gumi na Nijeriya.
Bayan an sako su daga tsare su ba bisa Æ™a’ida ba a watan Yulin 2021, gwamnatin shugaba Buhari ta hana ma’auratan fita Æ™asashen waje, inda ta hana su fasfo É—in su. Duk da bin hanyoyin doka domin dawo da fasfo É—insu, ma'auratan sun fuskanci tsaiko da gwamnati ta kitsa. A watan Janairun 2022, IHRC ta roÆ™i Majalisar ÆŠinkin Duniya, inda ta buÆ™aci Æ™ungiyar ta sa baki cikin lamarin.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata, a ƙarƙashin sabuwar gwamnatin shugaba Bola Tinubu, aka maido musu da takardun tafiye-tafiyen su, wanda hakan ya ba su damar neman magani a ƙasar waje.
Shaikh Zakzaky na fama da gubar harsashi a jikinsa, sakamakon raunin harbin bindiga guda hudu da dakarun ƙasar suka yi masa a shekarar 2015. An danganta gubar da harsasai da suka rage a jikinsa. Bugu da ƙari, Shehin malamin ya rasa ganinss a ido ɗaya, da yin amfani da hannu daya, kuma ya sha fama da da samun shanyewar jiki.
Ita ma Uwargidansa Malama Zeenah tana fuskantar matsalolin rashin lafiya da suka haɗa da cutar hawan jini da rashin iya tsayuwa da ƙafafu sakamakon harsashin da ya same ta a kusa da ƙashin bayanta, wanda hakan ya hana ta tafiya.
Kisan gillar da aka yi a Zariya a shekarar 2015 ya yi sanadin asarar rayuka sama da 1000 a tsakanin magoya bayan Harkar Musulunci. Duk da yawan mutanen da aka kashe, babu wani jami’in da aka gurfanar da shi ko kuma aka yi masa shari’a kan kisan.
Kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa na gudanar da bincike na shararbfage kan kisan kiyashin, a cewar IHRC.
No comments