Daga Ammar Muhammad Rajab Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; babbar Darakta a Kamfanin Dangote, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; babbar Darakta a Kamfanin Dangote, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta faɗa wa manema labarai cewa sun sayar da kamfanin da ke sarrafa kayan abincin tsawon shekara biyar da suka wuce. A don haka ba su da hannu wajen tsawwala farashin kayayyakin abinci a Nijeriya.
Fatima ta ce; "A gaskiya mun jima da sayar da fulawa ga kamfanin Olam. Wataƙila ba mu yaɗa labarin bane da kyau. A yau ya kai shekara biyar da muka siyarwa da Olam kamfaninmu da ke sarrafa abubuwa kamar fulawa, taliya, semovita, baki ɗaya duk ba namu bane. Amma da sunayenmu kuke ganinsu a kasuwa. Saboda daga cikin yarjejeniyar da muka yi da kamfanin da muka siyarwa za su ci gaba da amfani da sunan mu zuwa wani lokaci", ta labarta.
Ta ci gaba da cewa; "Yakamata a ce nan da shekara ɗaya haka su daina amfani da sunan. Amma duk kayan fulawa da kuke gani a kasuwa, ba na Ɗangote Group bane. Mun siyarwa da Olam kamfanin shekara biyar ke nan yanzu.
Da take bayanin dalilin da yasa har yanzu ake ci gaba da sarrafa kayan da sunan su kuwa, ta ce; "Eh ana faɗa ne saboda a cikin yarjejeniyar da muka yi da su da muka tashi siyar musu da kamfanin, to shiyasa suka ci gaba da amfani da wannan sunan.
Sannan ta fayyace cewa; "A cikin harkar abinci abin da muke yi yanzu, suga ne da gishiri, su kaɗai muke yi sai kuma kayayyakin magi, sai shinkafarmu, shi ba mu fara ba, amma muna tsammani a cikin wannan shekarar ko shekara mai zuwa, insha Allahu za mu fara.
Ta kuma alaƙanta tashin farashin kayayyakin da zancen dala. "Ka san da yake a Nijeriya kusan abubuwa duk shigowa ake da su. To shiyasa dala na sama, dole harkokin gudanarwa su yi sama, to ka ga idan harkokin gudanarwa ya yi sama, ai babu sana'ar da take yin sana'a domin ta faɗi. Ai kowa na yi ne saboda riba ko ya ya ne ya yi ta. Wallahi don harkar wannan dala ɗin ce. Amma mu kan mu abin ba ya mana daɗi yadda farashi yake sama. Amma abu ne wanda ba mu da na yi a kai, amma insha Allahu na san Allah zai kawo mafita".
Ta ce sam matsalar ba daga gare su bane. "Muke sarrafawa amma kuma a dala muke siyowa. Daga inda muke siyowa ba sa sayar mana a Naira. Shi sukari ɗin da muke siyowa 'raw sugar' ɗin daga Brazil ake kawo shi. To ka ga a dala muke biyansu. Gishirinmu ma 'crude salt' daga Brazil muke kawo shi, shi ne matsalar. Komai shigo da shi ake yi. Simintin mu ne kaɗai ake yi a Nijeriya. Shi kuma simintin duk wani harkokin sarrafa siminti ya zama siminti a dala muke siyo shi. Gas a garin nan a dala muke siyo shi. Manyan motoci da muke kai wa kwastamomi, a Dala muke siyo ta a shigo da su. Kayayyakin motoci ne, tayoyi ne, komai a dala ce.
Sannan ta ƙaryata cewa farashin siminti ya kai dubu sha biyar, inda ta ce; "Mu ba mu da labarin ya kai dubu goma sha biyar. Sai dai idan kuma a kasuwa ne suke sama da farashin, amma mu dai a fanninmu ba mu da wannan masaniyar.
"Mun zauna da gwamnati kuma mun yarda cewa siminti ba zai shige farashin dubu bakwai ba zuwa dubu takwas. Wanda ya danganta da inda za a kai maka simintin. Akan wannan muka tsaya", ta ƙarƙare.
No comments