Daga Bello Hamza, Abuja Ministan ma’aikatar bunksa tattalin arzikin cikin Teku Adegboyega Oyetola ya sanar da cewa, Gwamnatin Ta...
Daga Bello Hamza, Abuja
Ministan ma’aikatar bunksa tattalin arzikin cikin Teku Adegboyega Oyetola ya sanar da cewa, Gwamnatin Tarayya za ta fara gyran tashoshin Jiragen Ruwa da ke Apapa da kuma na Tin-Can.
Oyetola, wanda ya sanar da hakan a ranar Alhamis ya ce, ana ana bukatar za a kashe dala miliyan 800 domin a fara yin wannan aikin.
Ministan ya bayyana hakan ne, a yayin Hukumar kula da Tasoshin Jiragen Ruwa (NPA),ta kaddamar da jaragen ruwa guda bakwai na yin sintiri a tashoshin Jiragen ruwan, inda ya ce, ana sa ran Jiragen ruwan za su taimaka wajen kara habaka aiki a tashoshin Jiragen ruwan na kasar nan.
A cewar Oyetola, ma’aikatarsa za ta yi dukkan mai yawa wajen ganin an rage yawan sundukan da ke a tasshoshin ruwan nan da kwanuka hudu, sababin kwanuka shida zuwa goma.
Ya yi nuni da cewa, ganin cewa yanzu ana tafiya da zamani ne, za a tabbatar da an mayar da tasoshin Jirgen ruwan zuwa na zamani don su tafi kafada da kafada da na sauran duniya.
A cewarsa, dole ne mu jinjina wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, bisa kirkiro da ma’aikatar ta kula da ta tattalin arziki na kasan ruwa tare da kuma bamu goyon bayan da ya dace.
Ya kuma yaba wa mahukunatan hukumar ta NPA kan karfafa tsaro a tekunan kasar, inda ya ce, ma’aikatar kadai ba za ta iya cimma burin da ta sa a gaba ba tare da an samar da tsaro a tashoshin jiragen ruwan kasar ba.
A jawabinsa tun da farko Manajin Darakta na NPA Mohammed Bello-Koko ya ce, an samar da Jiren ruwan bakwai ne domin a samar da tsaro a tashoshin Jiragen ruwan.
Ya ce, kaddamarwar ta yau ta nuna a zahiri kan kokarin da NPA ke yi na kara habaka ayyukanta, inda ya kara da cewa, kaddamar da Jiragen zai kara saita hukumar domin ta cimma burin da ta sanya a gaba, musamman wajen rage cunkoso tashoshin Jiragen ruwa na Onne da ke a jihar Ribas Warri da ta Kalaba.
No comments