Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rufe Gidan Damben Ali Zuma Akwai Sauran Rina Akaba - Sarakuna Yankin

Daga Hussaini Yero  Iyayan alumma Sarakuna sun maganta bayan sati biyu da rufe gidan Danben Diye-Diye zuwa Dakwa na Ali Zuma ind...


Daga Hussaini Yero 

Iyayan alumma Sarakuna sun maganta bayan sati biyu da rufe gidan Danben Diye-Diye zuwa Dakwa na Ali Zuma inda suka bayyana cewa,akwai sauran runa Akaba kuma tamkar kashe maciji ne ba a sare kansa ba.

Mai Martaba Sarkin Dakwa Dr Alhassan Babachiri ya jinjina ma jami'an tsaro akan rufe gidan Danben Diye-Diye zuwa Dakwa da ya zama tarnaki ga al'umar yanki ta bangaren tsaro.

A jawabin sarakunan ga manema labarai Sarkin Dakwa ya bayyana cewa,akwai gidajan da ake tafka laifuka da dama a ya kin Masarautar sa akan haka ya ke kira ga Jama'a da su bayyana mana su dan sanar da Jami'an Tsaro dan daukar mataki akai.inji Sarkin Dakwa Alhassan".

"Dan rufe Gidajan da suka bayyana a Fili akwai masu yawa a boye cikin aluma tamkar kashe macijine baa sare Kansa ba inji Basaraken.

Sarkin Dakwa Alhassan ya Kuma yiyikira ga Gwamnatin da ta duba da halin da al'umma ke ciki na matsin rayuwa dan kawo masu dauki cikin gaggawa ba sai sun jikataba .kuma yayi kira ga Jama'a da sucigaba da yin addua dan samun dorewar zaman lafiya a kasa baki daya .

Dagacin Diye-Diye Alhaji Sa'idu Hamza Sani shima yayi kira ga gwamati da ta sanya idanu akan masu Hana alumma walwala a Diye-Diye musamman rufe gidan Danben Diye-Diye zuwa Dakwa alheri ne a garemu da jama'ar dan suna takurawa Jama'a masu laifuka suna fakewa da gidan domin cutar da alumma.dan haka rufe gidan Danben yayi dai dai kuma Jami'an Tsaro sunyi abunda ya dace a lokacin da ya dace .

Shikuwa Sarkin Malaman Abuja Muhammad Alkwandawi ya jinjina ma jami'an tsaro Abuja da cewa,lallai babu wanda ya gagare su dan yadda Mai gidan Danben ke tinkaho da fariya sai gashi cikin dare daya Jami'an Tsaro suntarwatsa gida kuma sun kama mutane da dama masu manyan laifuka.inji Sarkin Malaman Alkwandawi."

"Shek Alkwandawi ya kuma tabbatar da cewa,gidan Danben Ali Zuma ya dakile harkar kasuwanci da cigaban alumma musamman filaye da ke kusa gidan sungagar ginawa ga  màsusu.kuma babu dare ko rana barayi nashiga  gidajen mutane dan yanzu haka sun shiga gida na sun kwashe kayan da ke cikin.kuma dama kafito da wayar ballantama kace zaka saida Fili ko gida sai kayi asara sabo da yadda gidan Danben ya kawo matsala rashin  Tsaro a yankin.

Akan haka ne muke Kara kira ga Jami'an Tsaro da su cigaba da farautar masu ruwa da tsaki na gidan Danben Dan dakile matsalar cutar da alumma da gidan ke haifarwa .Allah ya taimaki Jami'an Tsaro mu wajan yakin da duk wani baragurbi da yake takurama alumma aduk inda ya ke .

No comments