Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Muna tsare da shugabannin Binance a Nijeriya'

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa BBC cewar tana tsare da wasu manyan jami'an shafin hada-hadar kuÉ—in kirifto na Binance a birnin Abuja....



Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa BBC cewar tana tsare da wasu manyan jami'an shafin hada-hadar kuÉ—in kirifto na Binance a birnin Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da suka ɓulla a daren ranar Laraba da ke nuna cewa hukumomi na tsare da jami'an.

A wata tattaunawa da BBC, Zakari Mijinyawa, wanda shi ne shugaban sashen yaɗa labaru na ofishin mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, ya ce "ana yi wa jami'an tambayoyi ne ƙarƙashin binciken da hukumomin tsaro ke yi kan daidata kasuwar musayar kuɗi, wanda ofishin na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ke jagoranta".

Hukumomi na zargin shafin na Binance ne da laifin "ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje a ƙasar".

Darajar takardar kuɗin Najeriya dai ta yi faduwar da ba a taɓa gani ba a tarihi tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ƙyale kasuwa ta tantance darajarta.

Lamarin ya ƙara jefa tattalin arziƙin Najeriya da kuma al'umma ƙasar cikin garari, abun da ake ganin ya samo asali daga cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Zakari Mijinyawa ya shaida wa BBC cewa "yanzu haka akwai tattaunawa da kuma yarjejenyoyi da ake yi da jami'an na Binance, kuma suna bayar da haÉ—in kai."

Sai dai jami'in bai yi wa BBC cikakken bayani kan tsawon lokacin da za a ɗauka ana binciken, ko kuma yarjejeniyar da ake son ƙullawa ba tsakanin gwamnati da shafin na Binance.

Gwamnan Babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa kusan dala biliyan ashirin da shida na bi ta Binance ta hanyoyi da masu amfani da manhajar da ba za mu iya tantancewa ba".

A hira da gidan Talabijin na Channels, Bayo Onanuga, kakakin fadar shugaban ƙasa ya zargi manhajar kirifto da sa farashin kuɗin waje a ƙasar tare da karɓar matsayin babban bankin.

"Idan ba mu fatattaki Binance ba, Binance zai durƙusar da tattalin arzikin wannan ƙasa. Kawai suna ƙayyade farashin," kamar yadda ya bayyana.

Kawo yanzu dai jami'an kamfanin na Binance ba su ce komai ba kan kamen.

A disamban bara ne hukumomin Najeriya suka ɗage haramcin shekara biyu da aka ƙaƙaba kan hada-hadar kirifto saboda abin da suka kira haɗarin ɗaukan nauyin almundahana da ta'addanci daga kamfanin kirifto a ƙasar.

A 2021, gwamnati ta rufe shafin AbokiFX, fitaccen dandalin da ke bayar da bayanai game da farashin kuɗin ƙasar waje kan zarge-zargen masu dandalin na ƙayyade farashin kuɗin waje tare da janyo karyewar darajar naira a kan dalar Amurka.

Matakin baya-bayan nan da gwamnati ta ɗauka na garƙame kamfanin Binance na daga cikin matakan da take ganin zai ceci Naira da darajarta ta faɗi da kusan kashi 70 cikin 100 cikin wata takwas da ya gabata.

No comments