Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dakatar Da Sanata Ningi Bai Mana Daɗi Ba - ACF

Ƙungiyar Tuntuba ta Arewacin Nijeriya ta nuna rashin jin dadinta game da dakatarwar da majalisar dattawar kasar ta yiwa sanata A...

Ƙungiyar Tuntuba ta Arewacin Nijeriya ta nuna rashin jin dadinta game da dakatarwar da majalisar dattawar kasar ta yiwa sanata Abdul Ningi, bisa zargin da ya yi na yin cushe a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekarar, da ya kai naira Tiriliyan 3 da miliyan dubu dari 7.

Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya a zauren majalisar dattawar Najeriya wanda kuma je shugabantar kungiyar sanatocin Arewacin kasar, majalisar ta dakatar da shi ne har na tawon watanni 3.

Toh sai dai a cikin sanarwar da sakataren yada labaran kungiyar ACF Farfesa Tukur Muhammad Baba ya fitar, ta ce dukkanin ababen da majalisar ke tuhumar sanata Ningi akai an gina sune bisa zargi, don haka ta ce bai kamata majalisar ta yi gaggawar daukar matakin dakatar da shi ba.

ACF ta ce kafin daukar irin wannan mataki da majalisar dattawar Najeriya tayi, kamata ya yi a samar da masu bincike na musamman don gudanar da binciken kwakwaf kan zarfin da Ningi yayi.

Kungiyar ta kuma ce da wannan mataki da majalisar ta dauka a kan dan majalisar, a yanzu yankin da yake wakilta bai san matsayinsa ba, duk da bukatar wakinci da yake nema a zauren.

Dama dai a wata zantawa da aka yi da Sanata Abdul Ningi ne, ya yi zargin cewar anyi cushe a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekarar, lamarin da ya sanya majalisar tabka mahawara akai, daga karshe kuma ta dauki matakin dakatar da shi.




No comments