Daga Hussaini Yero, Funtua A kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi na saukaka ma al'ummar jihar ƙarƙashin Ofishin Uwargidan gwamna D...
Daga Hussaini Yero, Funtua
A kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi na saukaka ma al'ummar jihar ƙarƙashin Ofishin Uwargidan gwamna Dauda Hajiya Huriya, ta ƙaddamar da bada tallafin abincin azumi da kayan sallah ga Magidanta dubu ashiri a faɗin jihar.
Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta ƙaddamar da rabon kayan a cikin wannan wata na Ramadan a ƙananan hukumomin Gummi, Bukkuyum, Anka, Talata Mafara, Bakura Da Maradun a yanzu haka.
Kayayyakin abincin da aka raba sun hada da Shinkafa, Gero, Masara na, Suga masara, Taliya, Wake, Man gyada da dai sauran su.
Uwargidan Gwamnan ta ƙara da cewa, gidaje dubu ashirin ne za su ci gajiyar tallafin a faɗin ƙananan hukumomi goma sha hudu.
Huriya Dauda ta yi kira ga masu rabon kayan da su ji tsoran Allah wajen rabawa kuma duk wanda muka samu da bata tsarin rabon lallai zai gamu da hukunci dai dai da abin da ya aikata. Kuma ta jaddada aniyar gwamnati na ci gaba da tallafawa al’ummar jihar.
Ta kuma buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci na azumin Ramadan wajen gudanar da addu’o’i Allah ya ba ikon kawo ƙarshen wannan hali da muka samu kanmu a ciki.
Kuma ta tabbatar da cewa, Maigidanta gwamna Dauda yana iyaka ƙoƙarinsa na sauke haƙƙin da ke kansa na wannan al'umma.
A nasa jawabin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Hon. Ahmad Garba Yandi ya tabbatar da cewa, wannan tallafin abincin Azumi da kayan sallah na daga cikin alƙawuran wannan gwamati a lokacin yaƙin zaɓe cewa, duk ɗan Zamfara zai dara idan muka samu nasara gashi ko a yau shaida kuke a kan haka.
Kuma duk wata gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda, muna raba magunguna ga asibitoci ƙananan Hukumomi sha huɗu da muke da su kyauta ne ake badawa ga mata da ƙananan yara, in ji Hon Garba Yandi.
Akan haka ne Hon. Yandi ya ƙara jaddada cewa, wannan gwamati na da shirye-shirye ga al'ummar jihar Zamfara na ci gaban ta. Kuma fatarmu shi ne Allah ya dafa mana mu cimma burin mu na ci gaban jiharmu ta kowanne ɓangare, Amin.
No comments