Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kamfanin Jaridun LEADERSHIP Ya Karrama Shehu Isma'ila Umar Almadda

Daga Idris Umar, Zariya Kamfanin Jaridun LEADERSHIP ya karrama Shehu Isma'ila Umar Almadda da kuma miƙa godiya bisa ƙoƙarins...

Daga Idris Umar, Zariya

Kamfanin Jaridun LEADERSHIP ya karrama Shehu Isma'ila Umar Almadda da kuma miƙa godiya bisa ƙoƙarinsa na shafe tsawon lokaci yana gabatar da shafin DAUSAYIN MUSULUNCI a Jaridar LEADERSHIP Hausa. 

Editan Jaridar LEADERSHIP Hausa, Abdulrazaq Yahuza Jere ne ya miƙa takardar karramawar tare da Shehu Yahaya Kaduna a madadin mahukuntan kamfanin. 

Mika saƙon karramawar ta gudana ne a ranar Juma'a 27 ga Sha'aban 1445 waccw ta yi daidai da 8/3/2024. 
 
Al'umma da dama ne suka miƙa saƙon godiyarsu ga kamfanin jaridar ta LEADERSHIP HAUSA bisa wannan ƙoƙari cikin su harda ƴan uwa da abokan arziƙi na zuriyar wakilin Jaridar ta LEADERSHIP HAUSA na shiyyar Zariya, Idris Umar da fatan zumuncin zai ci gaba.

No comments