Daga Hussaini Yero Bikin ranar mata ta duniya ta bana 2024, Uwargidan gwamnan Zamfara Huriyya Dauda Lawal ta ba mata Guragu 450 ...
Daga Hussaini Yero
Bikin ranar mata ta duniya ta bana 2024, Uwargidan gwamnan Zamfara Huriyya Dauda Lawal ta ba mata Guragu 450 tallafin kudi naira dubu talatin a faɗin jihar ta Zamfara.
Hajiya Huriya Dauda, a jawabinta ta bayyana cewa, a yau rana ce mai muhimmanci ga mata don rana ce da majalisar dinkin duniya ta warewa mata don su baje kolinsu da kuma tsara hanyoyin samun ci gaban su da shiga kowanne tsari don samun ingantacen rayuwarsu.
"A kan haka ne a yau ni da Maigidana gwamna Dauda muke yi wa matan jihar Zamfara albishir wajen sanya mata a kowanne sashe na gwamnati da bada mukamai da jindadi da walwalarsu a faɗin wannan jiha ta mu ta Zamfara", in ji Uwargida Huriya Dauda.
Huriya Dauda ta kuma tabbatar da gwamati su na tafiya kafada da kafada da kungiyoyin mata don samun nasara rayuwar su. "Kuma a yau ku shaida ne dan yanzu haka mutare da shugabar mata manoma da sarrafa amfani gona da kiwo ta jihar Hajiya Shemau Nalado wacce ita ma ta gabatar da jawabin ta a nan".
"A ƙarshe ina mai tabbatar muku da cewa, lallai Maigidana ya yi muku albishir na abubuwan more rayuwa da dama a gwamnatinsa ga mata, kuma mu masu cika alkawari ne ku shaida ne akan haka a cikin 'yan watannin da muka yi muna mulki.
"Rokon da muke maku a kodayaushe shi ne mu dage da addu'ar samun dawmammen zaman lafiya a wannan jiha da ƙasa baki ɗaya.
No comments