Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta haramta shirya fim ɗin da ke nuna fadan daba da harkar daudu a jihar. Shugaba...
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta haramta shirya fim ɗin da ke nuna fadan daba da harkar daudu a jihar.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan jim kadan bayan wata tattaunawa da ya yi da masu shirya fina-finan Kannywood, tare da wasu kungiyoyin da al'amarin ya shafa.
Shugaban ya ce biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al’umma k eyi a kan shirya fina-finan da ke nuna fadan daba da harkar daudu a Jihar Kano, ya bayar da umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan da ke nuna fadan daba da harkar daudu a faɗin jihar.
Ya ce doka ce ta bai wa hukumar tasa damar dakatarwa ko hana duk wani fim da ta ke ganin ya ci karo da tarbiyya tare da al’adar al’ummar jihar.
Ya ce lokaci ya wuce da za a sanya ido ana shirya irin wannan gurbatattun fina-finai da ke kokarin lalata tarbiyyar yara.
Wannan mataki da hukumar ta ɗauka dai yana da alaƙa da rikicin faɗan daba da ake fama da shi a unguwar Ɗorayi da ke Jihar Kano, inda a cikin wannan watan Ramadan aka kashe mutane da dama a unguwar.
Wasu a jihar sun koka kan ganin kallon fina-finan da suke nuna faɗan daba wajen taka muhimmiyar rawa wajen karuwar fadace-fadacen daba a jihar.
Yanzu haka tunanin ya kasu biyu wasu na gani wannan mataki yayi daidai wasu kuma na fadin hukuncin yayi tsauri da yawa.
No comments