Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Barka Da Sallah: Saƙon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa Na Nijeriya

Shima a nasa sakon barka da sallah, babban hafsan rundunar sojojin kasa na kasar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukaci dakarun kasar ...


Shima a nasa sakon barka da sallah, babban hafsan rundunar sojojin kasa na kasar Janar Taoreed Lagbaja, ya bukaci dakarun kasar da su rubanya kokarin da suke yi wajen yaki da matsalar tsaro a fadin kasar.

Janar Lagbaja ya kuma ce irin kokarin da suke yi a yaki da ‘Yan ta’adda da ‘Yan bindiga da kuma ayyukan barayin man fetur ba zai tafi kawai ba, ya na mai jaddada bukatar da ke akwai ga Jami’an wajen kara kaimi a ayyukan da suke yi na wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Kazalika ya bukaci Dakarun kan su hada karfi da karfe da sauran jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu na kakkabe masu kawo tazgaro ga tsaron kasar.

No comments