Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Buƙaci 'Yan Nijeriya Su Haɗa Kansu Don Ciyar Da Ƙasar Gaba

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su hada kansu da kuma nuna halin sadaukar wa, don gudanar da aikin g...

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su hada kansu da kuma nuna halin sadaukar wa, don gudanar da aikin gina kasar.

A cikin sakonsa na barka da Sallah da mai taimaka masa wajen hulada da kafafen yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura wajen Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasar su dukufa wajen samar da hadin kai a tsakaninsu.

Shugaba Tinubu wanda ya taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murya, ya kuma yi addu’ar Allah ya amshi ibadun da suka gabatar.

No comments