Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bikin Sallah: Gwamna Dauda Lawal Ya Taya A'ummar Musulmi Murna

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya taya É—aukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Æ™aramar Sallah, tare da yin  kiran a ...


Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya taya É—aukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Æ™aramar Sallah, tare da yin  kiran a Æ™ara Æ™aimi wajen addu’o’in samun zaman lafiya a Zamfara da Nijeriya baki É—aya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce watan Ramadan ya ba da damar yin addu’ar neman taimakon Allah kan matsalar tsaron Æ™asar nan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya kamata al'ummar Musulmi su ci gaba da nuna kyawawan ɗabi'u da halayyen ƙwarai har bayan watan Ramadan.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bikin Æ™aramar sallah wani lokaci ne na farin ciki, domin yana nuna nasarar kammala azumi da kuma kusanci da Ubangiji da aka samu a cikin watan Ramadan mai alfarma.

“A ranar Idi, Musulmi suna nuna godiya ga lafiya da damar da ya ba su na sauke nauyin da aka É—ora musu na azumi.

“Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin biki don inganta zaman lafiya da nuna soyayya ga juna.

“Don magance matsalolin tsaro da Nijeriya ke fuskanta, dole ne mu sa ido ga juna, mu tsaya tsayin-daka kan addu’o’in mu, sannan mu mara wa Æ™oÆ™arin gwamnati baya na kawo Æ™arshen duk wasu masu aikata muggan laifuka.

“Ina taya É—aukacin al’ummar Musulmin Zamfara da Nijeriya da ma duniya baki É—aya murna. Da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya kuma cikin Æ™oshin lafiya,” in ji sanarwar.

No comments