Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hassan Musa Ya Amsa Kiran Fitowa Takarar Shugaban Karamar Hukuma Funtuwa A Jam’iyyar APC

Daga Hussaini Yero, Funtua Babban Sakataren mai ritaya a jihar Katsina, Alhaji Hassan Musa Anda ya amsa kiran al'ummarsa na yin takarar ...


Daga Hussaini Yero, Funtua

Babban Sakataren mai ritaya a jihar Katsina, Alhaji Hassan Musa Anda ya amsa kiran al'ummarsa na yin takarar shugaban karamar Hukumar Funtuwa da ke jihar Katsina, karkashin jagorancin Jam'iyyar APC a zabe mai zuwa 2025.

Hassan Musa Anda ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 19/04/2024 a dakin taro na marigayi Sarkin Alhazai dake Jabiri cikin karamar hukumar Funtuwa .

Dan takarar ya bayyana cewa, shi mutum ne na jama'a kuma ba zai watsa ma duk mai son shi da abin alheri kasa a fuska ba , a don haka ya ga ya dace ya amsa kiran masoyansa na fitowa takarar Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa a zabe mai zuwa da yardar Allah; "na san akwai 'yan takara da yawa amma jama'a sune alkalai za su zabi wanda yafi cancanta.kuma wannan takara ban dauke ta ko a mutu ko a yi rai ba", in ji Hassan Musa Anda.

Hassan Musa ya yi kira ga magoya bayansa da su yi biyayya da tsarin kundin jam'iyyar da yada manufofin mu na alheri ba tare da bata wani dan takarar ba.

Hassan Musa Anda ya yi kira ga al'umma kamarar Hukumar Funtuwa da na jihar Katsina baki daya da su ci gaba da addu'a ga gwamnatin gwamna Dikko Radda don ganin kudirinsa ya hakkaku na samun Zaman lafiya da ci gaban jihar mu da kasa baki daya.

A na su jawaban shugabanin tafiyar, Alhaji Nura Sule 'Yan Daki da Muntari Lawal Miloniya Maska, sun bayyana salilansu na ganin Hassan Musa ya cancanci ya zamo Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa da dalilan su kamar haka".

"A wannan lokaci babu wandanda ya fi Hassan Musa cancanta zamowa dan takarar shugaban Karamar Funtuwa, saboda yadda ya san ta gaba da baya,dan Hassan Musa ya Kwashe tsawon Shekaru 20 ya rike da mukamin Shugaban Ma'aikata na Karamar Hukumar Funtuwa,sannan ya zamo Darakta Mulki sannan kuma ya rike Mukamin na karshe a Matakin Karamar Hukumar Watau (DAF) .

Hassan Musa Anda ya zamo kantoman Kananan Hukumomin , Dandume,Safana, Kankara da Karamar Hukumar Sabuwa.dan haka kwararene a sanin Mulki na Karamar Hukumar ta kowane sashe.

Haka kazalikama , Hassan Musa ya zamo Babban Sakataren na Dum-dumdum ,a ma'aikatun Jihar Katsina wanda a nan yayi ritaya.

Dan haka wadannan dalilai namu sune muka dogara da su na kwarewar sa da jajircewarsa wajan tafiyar da Mulki, yasa muka huramasa wuta akan ya fito yayi takara a Jamiyyar mu ta APC dan ya tsamo Karamar Hukumar Funtuwa daga mawuyacin halin da muke ciki".Inji Kwamandojin yakin Neman Zabe Hassan Musa Anda,Alhaji Nura Suleman da Muntari Maska Miloniya.

No comments