Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƴan Sandan Kenya Sun Cafke Shugaban Binance Da Ya Tsere Daga Nijeriya

Rudunar ƴan sanda a Kenya ta kama jami'in kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla yayin da hukumar ƴan sanda ta duniya, Interpol ke neman ti...



Rudunar ƴan sanda a Kenya ta kama jami'in kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla yayin da hukumar ƴan sanda ta duniya, Interpol ke neman tisa ƙeyarsa zuwa Najeriya a wannan makon.

Majiyoyi daga gwamnati da suka san da shari'ar waɗanda suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana kan batun sun tabbatar da labarin ga ƴan jarida.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce ƴan sandan Kenya sun kama shugaban kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla kuma Interpol za a tisa ƙeyarsa zuwa Najeriya a makon nan.

Wata majiyar ta ƙara tabbatar da kama Anjarwalla a Kenya.

Bayanai na cewa gwamnatin Najeriya ta gano Anjarwalla a Kenya sakamakon tserewar da ya yi daga inda aka tsare shi a Najeriya.

Hukumar EFCC da Interpol da rundunar ƴan sandan Kenya sun zurfafa tattaunawa domin hanzarta tisa ƙeyar Anjarwalla zuwa Najeriya.

No comments