Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga kwamitin tabbatar da tsaro a karamar hukumar Chanchaga da su tabbatar sun gudanar da aikin su bi...
Daga Awwal Umar
Kontagora
An yi kira ga kwamitin
tabbatar da tsaro a karamar hukumar Chanchaga da su tabbatar sun gudanar da
aikin su bisa tsarin doka, duk wanda aka cafke da zargin ta'addanci a tabbatar
an dauki cikakken bayaninsa tare da gabatar da shi gaban kuliya cikin awanni
arba'in da takwas domin akwai kotunan musamman da gwamnati ta kafa wajen
hukunta duk wanda aka kama.
Kwamishinan shari'a
kuma Alkalin Alkalai na jihar Neja, Hon. Nasiru Mu'azu ne ya yi kiran kaddamar
da kwamitin a fadar Sarkin Minna, Mai Martaba Umar Faruq Bahago a yammacin Talatar
nan.
A cewarsa tattara
bayanan mai laifi zai bada damar duk wani lokacin da aka samu rahoton
ta'addanci za a samu sauke cafke duk wanda ake zargin yana da hannu domin akwai
cikakken bayani a kan sa.
Da yake bayani ga
manema labarai, shugaban kwamitin, tsohon kaftin din soja, Umar Sanda ya ce
kwamitinsa a shirye take ta yi aikin ba sani ba sabo, duk wanda aka cafke shi
da laifin ta'addaci wajibi ne ya fuskanci hukunci.
Kaftin Sanda, ya cigaba
da cewar a baya ana zargin wasu masu ido da kwalli kan yi amfani da matsayinsu
wajen karbo belin masu laifi, a wannan karon ba za mu sanya idanu hakan ya ci gaba
da faruwa ba, matakin farko na aikin mu za mu tabbatar mun wayar da kan matasa muhimmancin
zaman lafiya, shi yasa a wannan zaman muka gayyaci iyaye da masu ruwa da tsaki
dan wayar masu kai kan yin katsalandan a ayyukan mu, duk yaron da aka kama dole
ne a hukunta shi, za mu samar da tsare tsaren tsaro ta yadda za mu tabbatar
ta'addanci bai samu gindin zama a Minna ba.
Hon. Mohammed Nma Kolo,
Jawon Minna, shi ne mai baiwa gwamnan Neja shawara akan harkokin siyasa da
tsare tsare, yace yanzu ba lokacin siyasa ba ne, balle wani mai laifi ya labe
da sunan siyasa.
Da zaran an gama zabe
siyasa ya kare wajibi kowa ya hada kai da gwamnati dan ganin an samu cigaban
kasa, ba wani dalilin da zai sa mutum ya dauki mataki yana farautar jama'a, ana
zubar da jini tare da kashe rayukan jama'a da yin sace sace.
Duk wanda ya sanya
hannu wajen ganin an sake mai laifi wannan tamkar daurewa laifuka gindi ne, dan
haka gwamnati ba za ta lamunci duk wani dan siyasa ko wani babban mutum sanya
hannu wajen sake mai laifi ba.
Ina kira ga matasa da
su sani su ne manyan gobe, ba yadda goben su za ta yi kyau mutum ba su gyara
rayuwarsu a yanzu ba.
Kamar yadda aka
bayyanawa mai martaba sarkin Minna yanzun akwai aikace aikace da dama da
kwamitin za ta gabatar dan samar da zaman lafiya tare da kawo karshen sara suka
da kashe jama'a a garin Minna.
Kwamitin dai ya shafi
masu rike da Sarautun gargajiya, ‘yan siyasa da jami'an tsaro don ganin an
samar da zaman lafiya a Minna.
No comments