Ministan sufuri a Najeriya, Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na ...
Ministan sufuri a Najeriya, Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana.
Hakan na zuwa ne kwana É—aya
bayan da jirgin kamfanin ya zame daga titin jirginsa a tashar jirgin sama ta
Murtala Muhammed da ke Legas.
Gidan talabijin na
Channels ya ruwaito ministan ya kuma umarci a gudanar da bincike kan kamfanin.
Binciken zai shafi dukkan matakan kariya da hanyoyin yin gyara domin tabbatar
da cewa kamfanin yana bin umarnin ƙa'idojin tafiyar da harkar sufurin jirage.
Acikin wata sanarwa da
aka aikewa darakta janar na NCAA, minsitan ya ce matakin ya zamo wajibi domin
tabbatar da cewa kamfanin yana bin ƙa'idojin aiki musamman na matakan kariya.
Jirgin Dana É—auke da
fasinja 83 da ya taso daga Abuja zuwa Legas ya zame daga kan titinsa ranar
Talata.
No comments