Daga Awwal Umar Kontagora Al'ummar Kontagora sun yabawa yan majalisun dokokin jiha masu wakiltar Kontagora ta daya da ta biyu, Hon. Muha...
Daga Awwal Umar Kontagora
Al'ummar Kontagora sun yabawa yan majalisun dokokin jiha masu wakiltar Kontagora ta daya da ta biyu, Hon. Muhammad Sani Umar da Hon. Abdullahi Isah kan yunkurin samar da tallafin kayan abinci abinci daga gidauniyar Dangote, tallafin wanda aka yi rabonsa cikin satin nan karkashin gidauniyyar Musulmi ta Muslims Foundation.
Tallafin wanda aka rabar da shi ya shafi yankunan da aka fi samun tagayyara bisa yanayin tsadar rayuwa da ake ciki.
Da yake amsa tambayoyin wakilin Madogara, dan majalisa mai wakiltar Kontagora ta biyu, Hon. Abdullahi Isah, ya ce shi da dan uwansa Hon. Sani Umar daya ne, domin sun zo majalisa ne bisa zabin al'ummomin da suke wakilta, saboda haka ba su tsaya kan yin dokoki ba, sun nutsa wajen shige da fice duk wani alherin da ake son ya kai hannu mabukata al'ummar su ta amfana.
Mun samu labarin gidauniyar Dangote ta ware abinci da tallafawa talakawan kasar nan, muka isar da bukatar dan al'ummar mu su amfana, ba mu amince a yi rabon a karkashin mu ba gudun kar siyasa ta shigo, muka amince da a damka a kalar rabon karkashin gidauniyar Muslims Foundation, kuma duk inda aka bayar wuraren da suka dace ne.
Ganin muradun gwamnatin jiha bisa jagorancin Manomi Umar Mohammed Bago na samar da sabuwar jihar Neja, ta hanyar karfafa guiwar manoma da samar da tsaro, samar da ayyukan raya kasa da zasu anfani jama'a muka dacewar dunkulewa wuri daya don yin aiki tare ta yadda al'ummar da muke wakilta za su ci moriyar mulkin dimukuradiyya.
Bada jimawa ba dai, majalisar dokokin jiha ta jefa kuri'ar amincewa da kudurorin gwamnati na samar da sabon sauyi ta hanyar ayyukan raya kasa, bunkasa harkar noma da tsaro.
A kan haka, dan majalisar ya sha alwashin karfafa guiwar jami'an tsaro na Bijilanti ta hanyar daukar nauyin gina sabon ofis mallakin Bijilanti a yankinsa.
No comments