Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NURTW Ta Koka Kan Hauhawar Farashin Man Fetur A Arewacin Kasar Nan

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar direbobin kananan motocin sufuri (Nigeria Union Road Transport Workers) ta koka kan tsadar hauhawar man f...


Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar direbobin kananan motocin sufuri (Nigeria Union Road Transport Workers) ta koka kan tsadar hauhawar man fetur a wasu yankunan jihohin kasar nan, wanda ta bayyana cewar ya kamata dilolin man fetur su tausaya talakawan kasa, musamman yadda gwamnati ta karya farashin man zuwa dari biyar da doriya.

Shugaban kungiyar a jihar Neja, Malam Garba Musa Bala ne ya yi koken ga manema labarai, ya ci gaba da cewar yanzu babu tsayayyen farashin man fetur a jihar Neja, misali a cikin garin Minna wasu gidajen mai a ranar Alhamis suna siyar da mai akan naira dari bakwai da arba'in zuwa da sittin, idan ka nausa wasu jihohin arewa farashin ya nunka hakan.

Yanzu idan ka shiga jihohin kudu da yawan gidajen mai suna sayar da man fetur akan naira dari biyar da arba'in zuwa shida da arba'in, wanda dukkanin wadannan masifun akan talaka yake karewa. Akwai bukatar dilolin man mu su yi kyakkyawar nazari su tausayawa rayuwar talaka maimakon jefa shi cikin ukuba.

Da ya juya bangaren direbobi kuwa, ya ce NURTW ta dubi tsadar rayuwa na hauhawar kayan gyaran mota da man fetur, karin kudin mota da su ka yi bai taka kara ya karya ba, inda mun yi la'akari da irin ukubar da direbobi ke sha akan tsadar man fetur da kayan gyaran mota da kusan sufuri ya tsaya cak a jihar nan.

Bala Musa, ya ci gaba da cewar a baya muna korafi akan matsalar hanya, yanzu matakan aikin gyaran hanyoyin jihar nan da gwamnati ta sanya a gaba, idan aka ci gaba kafin tsayawar ruwan sama ka'in da na'in muna kyautata za a samu sauki tafiya akan hanyoyin jihar nan.

Jihar Neja dai kusan ita ce cibiya kuma mahada mafi girma a kasar nan, domin duk wanda ya taso daga yankin arewa masu yamma da suka kunshi jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara, zuwa jihohin arewa masu gabas mafi sauki su biyo ta jihar Neja, amma gwamnatin da ta shude ba ta mayar da hankali akan gyaran su ba kamar yadda wannan gwamnatin mai ci ta himmantu ba.

Kamar yadda muka ga an mayar da hankali yanzu akan gyaran su muna kyautata zaton kafin wani lokaci matsalar lalacewar hanyoyi a jihar nan zai zama tarihi.

Shugaban ya bukaci gwamnatin mai ci da ta kara azama da himma wajen cigaba da ayyukan raya kasa, domin ba kasar da za ta cigaba muddin ba a inganta hanyoyin sarafa ba, wanda kusan dukkanin wani abu da ake tinkaho da shi idan gwamnati ta yi abin da ya dace ba sai an je da nisa ba, jihar Neja za ta iya samar da su. 

No comments