Dakarun sojin Nijeriya sun ce sun yi wa maɓoyar 'yan ta'adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ƙananan hukumomin Damasak da...
Dakarun sojin Nijeriya sun ce sun yi wa maɓoyar 'yan ta'adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ƙananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno.
Wata sanarwa da mai magan da yawun sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya fitar, ta ce an kai wa 'yan ta'ddan hari ne ranar Talata 23 ga watan Afrilu.
Samamen na haɗin gwiwa tsakanin rundunar Operation Haɗin Kai da sojin saman Najeriya da kuma dakarun MNJTF, ya ragargaji sansanonin 'yan ta'ddan abin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu tserewa.
Sai dai Gabkwet ya ce 'yan ta’addan sun yi yunkurin far wa sojojin sashe na 4 na MNJTF a garin Lada da ke kan iyaka tsakanin jamhuriyar Nijar da Najeriya.
"Mun bi bayan 'yan ta’addan da suka tsere a kan babura 8, inda muka gano su a wurare 2 da ke kauyen Zarri, mai tazarar kilomita 28 daga gabashin Damasak da Mala Alide a karamar hukumar Mobbar ta Jihar Borno," in ji Gabkwet.
Ya ce an gano wani wuri da 'yan ta'addan suke ɓoye wa da baburansu a cikin Kauyen, karkashin bishiyoyi.
Baya ga wannan, dakarun Operation Haɗin Kai sun kuma kai hare-hare ta sama karkashin jagorancin jiragen leƙen asiri na ƙasar Nijar (ISR) a wuraren da 'yan ta'addan suke.
Hotunan sashen leƙen asirin sun tabbatar da cewa an kashe 'yan ta'adda da dama tare da lalata sansanoninsu.
Sojojin sun ce ƙoƙarin haɗin gwiwa da suke yi na haifar da sakamako mai kyau a ɓangarorin iyakar ƙasar.
Sun ce hakan ya janyo raguwar ayyukan ta'addanci da sauran laifukan da masu keta iyakokin ƙasar domin guje wa shari'a ke aikata wa.
No comments