Daga Ammar Muhammad Rajab Fitaccen Fasto din nan da ke kira ga wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin addinai, Fasto Yohanna Buru ...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Fitaccen Fasto din nan
da ke kira ga wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin addinai, Fasto
Yohanna Buru ya yi kira ga al’ummar musulmi da kirista a duk inda suke a fadin
Nijeriya da su rungumi hadin kai da zaman lafiya a tsakaninsu.
Fasto Yohanna Buru ya
bayyana hakan ne a yayin da wakilinmu yake zantawa da shi a Zariya, inda ya
jaddada bukatar da yake akwai na wanzar da zaman lafiya a tsakanin musulmi da
kirista. Inda ya ce; “ina kira ga al’ummar Nijeriya gaba daya amma ina da
magana da musulmi ne da kiristoci sune masu rinjaye a kasarnan. Kuma yawan
fitintinu na yawan faruwa a junansu. Ko
rashin yarda ne ko siyasa ne ya shiga ko rashin fahimtar addini ne ko ba a ilmantu na yadda za a yi zama a kyauta
mu’amala da zamantakewa a nuna wa juna kaunar juna, shi ne ya kai ga hakan.
Ya ci gaba da cewa; “ina
rokon Allah Ubangiji a cikin hikimarsa da ikonsa ya sa musulmi da kirista su
fahimci juna. Domin sune za su zama misali ga sauran masu addinai. Sai kuma a
samu mune ba ma zaman lafiya.
“Ya kamata masu
littafin Attaura da Zabura ya fito ya nuna misali bisa koyarwar littafi mai
tsarki, haka kirista haka musulmi. Duka wadannan ‘ya’yan Annabi Ibrahim ne,
kuma masu bin addinin Annabi Ibrahim ne. Ya kamata su zama misali.
A don haka ya yi kira da
a zauna lafiya da kowanne mutum; “Idan ma gado ne, to za a raba gado. A bar
fada da juna, a gina kasa, a gina juna, a yi taimakekeniya a fahimci juna, a
kaunaci juna, a yi gudu tare a tsira tare, shi ne mafita ga addini. Amma ‘yan
kananan abubuwan dake raba mu, abubuwan da suka hada mu sun fi yawa. A zauna
lafiya ko’ina a Nijeriya”, ya jaddada.
![]() |
Fasto Yohanna Buru a yayin tattaunawar. |
Sannan ya yi na musamman a Nijeriya ga masu tada kayar baya suna kashe-kashe da garkuwa da jama’a da su ji tsoron Allah su bari a zauna lafiya da juna; “Ina kuma rokon wadanda suke dauke da makamai, don an yi musu rashin adalci, ko ‘yan Boko Haram ne, ko kuwa masu garkuwa da mutane ne, ko kuwa wadanda ake cewa ‘yan fashin daji, muna rokon Allah su tausayawa talakawa, a zauna lafiya.
“Kuma a yi adalci a kowanne mataki. Idan Musulmi ne ka yi masa adalci. Idan kirista ne ka yi masa adalci, ita ce mafita ita ce zaman lafiya. Kuma mu koma ga Allah mu yi tuban gaskiya. Don mun riga mun saba ma Allah.
No comments