Daga Awwal Umar Kontagora Dan majalisar dokokin jiha, mai wakiltar Kontagora II, Hon. Abdullahi Isah ya biyawa dalibai 42 kudin jarabawar WA...
Daga Awwal Umar Kontagora
Dan majalisar dokokin jiha, mai wakiltar Kontagora II, Hon. Abdullahi Isah ya biyawa dalibai 42 kudin jarabawar WAEC da NECO a yankin da yake wakilta.
Dan majalisar ya cigaba da cewar bayan kudin jarabawar yana da kudurin bada tallafi akan masu matsalolin rashin lafiya, yace wadannan abubuwan guda biyu ba abu ba ne da za a yi sanyin guiwa akan su ba.
Ko a cikin wannan satin dan majalisar ya biyawa yara guda biyu kudin aikin Idanu a asibirin Idanu da ke kaduna.
Wani dan siyasar da ya nemi a sakaya sunan sa, yace da farko bai yi Abdullahi Isah ba, amma matakan da dan majalisar ke dauka yanzu matakai ne da ba sai ya tallata kan shi ba a gurin jama'arsa ba.
Mun yi yan majalisu da dama a yankin nan, maganar gaskiya duk da yanayin da ake ciki muna ganin irin abubuwan alheri na raya kasa da al'umma da dan majalisar nan yake yi. Wanda rawar da yake takawa yanzu ya nuna cewar an samu sauyi a siyasar Kontagora II.
Dan majalisar dai, yace jama'a ne suka zabo shi, kuma yana aikin ne dan su. Ba maganar ilimi da kiwon lafiya kadai ba, muna da kudurce kudurce da dama a gaba, idan Allah ya ba mu ikon aiwatarwa jama‚a ne da kan su zasu yi bayani wa duniya.
Ina dai kara jawo hankalin al'ummata da su cigaba da baiwa gwamnatin goyon baya, akwai kudurce kudurce da dama da gwamnatin Hon. Bago ta shirya na cigaban kasa da za mu anfana da shi a gaba.
No comments