Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Dokokin Neja Ta Fara Rangadin Rukunan Gidajen Maikunkele Da Three Arm Zone

Daga Awwal Umar Kontagora A cigaba da sanya idanu akan kaddarorin gwamnatin Neja, domin tabbatar da ingancin su, mataimakin shugaban kwamiti...



Daga Awwal Umar Kontagora

A cigaba da sanya idanu akan kaddarorin gwamnatin Neja, domin tabbatar da ingancin su, mataimakin shugaban kwamitin kula da ayyuka da inganta jihar, Hon. Abdullah Isah ya jagoranci mambabin kwamitin dan gani da ido akan yadda aikin rukunin gidaje na 3 Arm da rukunin gidaje na Maikunke suke ciki.

Kwamishinan gidaje da inganta jihar, Hon. Abubakar Umar Abule, da babban daraktan kula da tsarin gine gine, Hon. Bashir Yakubu Harka suna da cikin wadanda suka jagoranci yan majalisar dokokin da tabbatar da yadda ayyukan ke tafiya zuwa yanzu.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, mataimakin shugaban kwamitin na majalisar dokoki, yace ziyarar ta mu ta biyo bayan tabbatar da aikin yadda yake tafiya, dan tabbatar da ingancinsa ta yadda wadanda zasu anfana da gine ginen da su yi alfahari da irin kokarin da gwamnatin jiha tayi kan wadannan ayyukan. Dan haka mun bukaci masu ruwa da tsaki a jiha, yan kwangila da injiniyoyi su bada shawarwarin da zai kawo mana cigaba idan har akwai shi.

A matsayin mu na wakilan jama'a, mun sha alwashin tabbatar da adalci wajen sanya idanu akan kudaden jama'a da jiha ke kashewa, dan samar da kyakkyawar sakamako kamar yadda muka yi alkawali. Ziyatar ta mu ya biyo bukatar mu na sanya idanu akan tsare tsaren gwamnatin jiha na samar da ingantattun gidaje a jihar Neja.

Ina farin cikin samun kaina a daya daga cikin yan kwamitin nan, ta yadda zan nuna kulawa ta wajen inganta rayuwar al'umma wajen ganin an samu ingantattun tsarin gidaje a jihar nan.

Wadannan rukunin gidajen da gwamnatin Umar Bago ta gada an faro su ne tun lokacin mulkin Babangida Aliyu Talban Minna, wanda gwamnatin da ta gaje ta tayi watsi da su tsawon shekaru takwas sai bayan dawowar gwamnatin Umar Bago ta sake dawo da hankali wajen tabbatar da an kammala su.

No comments