A ci gaba da ayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da na Kansiloli dake ci gaba da gudana a jihar Bauchi a yau Asabar 17 ga w...
A ci gaba da ayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da na Kansiloli dake ci gaba da gudana a jihar Bauchi a yau Asabar 17 ga watan Agustan 2024, Samira Shu'aibu Maikano daga jam'iyyar Young Progressive Party (YPP) daga gundumar Wandi a ƙaramar hukumar Dass ta lashe zaɓen Kansila.
Madogara TV/Radio ta labarto cewa; Samira Shu'aibu ta samu ƙuri'u 1610, a yayin da Bashir Abdullahi daga jam'iyyar PDP ya zo na biyu da ƙuri'u 1352 sai Abdulwahab Aliyu daga APC da ƙuri'u 230.
No comments