Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jakadun Matasan APC Na Kasa Sun Nemi Shugaba Tinubu Ya Mika Jagorancin Jam'iyyar Ga Sanata Almakura

Daga Awwal Umar Kontagora Jakadun matasan APC na kasa (APC Youth Ambassadors) ta nemi shugaban Ahmad Bola Tinubu da ya mika jagorancin jam...


Daga Awwal Umar Kontagora

Jakadun matasan APC na kasa (APC Youth Ambassadors) ta nemi shugaban Ahmad Bola Tinubu da ya mika jagorancin jam'iyyar APC ga tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Umar Tanko Almakura.

Matasan sun bayyana hakan a wata takardar manema labarai da ta fitar yammacin yau asabar a Abuja, wanda shugaban matasan Engr. Kabiru Abdulhamid ya sanyawa hannu.

Takardar ta cigaba da cewar duba da irin gudunmawa da rawar da tsohon Sanatan ya taka tun lokacin jam'iyyar CPC har zuwa hadewar ta da sauran jam'iyyu inda aka samar da APC zuwa yanzu ba a nuna masa diyauci ba, lokaci ya yi da za a damka jam'iyyar ga dattijo kuma kwararre a siyasa wanda ke da kudurin ciyar da tsarin dimukuradiyya gaba.

Ya cigaba da cewar tsohon sanatan wanda ya fito daga yankin arewa ta tsakiya, yana gogewa ta siyasa, ya taba zama dan majalisar dattijai kuma ya zama gwamnan jihar Nasarawa har karo biyu, sannan ya kafa harsasai a dukkanin sassan kasar nan, wanda kwazon sa da bajintarsa ne yasa jam'iyyar APC da ke adawa a baya ta zama yau ita ke rike da madafun ikon kasar nan.

Ya kamata, mutumin da ya taka rawa irin wannan, kuma ya bada gudunmawar da ake cin anfaninta a yau, ya zama shi ne sahun gaba a tafiyar da shugabancin jam'iyya, domin shi yasan tudu da gangarar da yabi wajen ganin APC ta zama uwa a nahiyyar Afirika.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar ita wannan kujerar ta shugabancin jam'iyyar APC a matakin kasa, yankin arewa ta tsakiya ne ke da hurumin rike ta ba yankin arewa ta gabas da ke rike da ita yau ba.

Matasan suka ce indai cecekucen da ake yi ne na shugaban jam'iyyar APC a matakin kasa ba wanda yafi cancanta da dacewa wajen rike wannan kujerar tamkar Sanata Umar Tanko Almakura, a cewar takardar. 


No comments