Daga Awwal Umar Kontagora Dan majalisar dokokin jiha, mai wakiltar Kontagora II, Hon. Abdullahi Isah (Audun Mama) shugaban kwami...
Daga Awwal Umar Kontagora
Dan majalisar dokokin jiha, mai wakiltar Kontagora II, Hon. Abdullahi Isah (Audun Mama) shugaban kwamitin harkokin addinai kuma mataimakin shugaban kwamitin kula da gidaje da tsare tsare a jihar Neja, ya sha alwashin cigaba da tallafawa al'ummar da yake wakilta ta bangaren ilimi, kiwon lafiya da sana'a.
Dan majalisar ya sha alwashin hakan ne a lokacin da aka bijiro ma shi da wata badakalar filayen gona a yankin da yake wakilta.
Dan majalisar yace a koma a dokokin kasa, a dubi dokar tsarin mallakar fili, amma ba zai yiwu mu zura idanu wasu saboda biyan bukatar kansu su haddasa wa al'ummar mu fitinar da ba wanda ya san inda za ta dosa ba, duk hanyoyin da ya kamata majalisar dokoki da gwamnatin jiha za su bi za mu tabbatar an yi adalci ga kowa, muna da korafe korafen jama'a da dama a gaban mu kuma za mu tabbatar a matsayin mu na masu doka mun bi su sau da kafa ta yadda gwamnatin jiha za ta samu damar tafiyar da ayyukan cigaban kasa ta yadda al'umma za su anfana.
Dan majalisar yayi kira ga sarakuna iyayen kasa, da su sanya idanu lungu da sako dan dakile batagari masu yiwa kasa zagon kasa. Sarakuna su ne iyayen mu kuma mu masu biyayya ne amma duk wani abinda da za a zo masu da shi su tabbatar sun warware shi dan gani gaskiyar al'amari.
Ɗan majalisar ya yabawa al'ummar Kontagora, da jihar Neja kan irin goyon baya da karawa gwamnatin jiha kwarin guiwa wajen tafiyar da ayyukan da ta sanya a gaba dan cigaban jiha tare da kudurin samar da sabuwar jihar Neja kamar yadda ta ayyana.
No comments