Daga Wakilinmu Babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar Bauchi, ta yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar a j...
Daga Wakilinmu
Babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar Bauchi, ta yi watsi da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar, inda ta bayyana shi a matsayin wani zagon kasa na wawure hakkin zabe da kuma izgili ga dimokradiyya.
DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta samu nasara a dukkan kananan hukumomin jihar 20 a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 17 ga watan Agusta.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar (BASIEC), Alhaji Ahmed Makama ne ya bayyana sakamakon zaben a daren jiya Asabar a ofishinsa.
A ranar Lahadi 18 ga watan Agusta ne ake sa ran za a rantsar da zababbun shugabannin da mataimakansu.
Sai dai da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar a ranar Asabar, mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Barista Rabi’u Garba, ya soki zaben, inda ya yi zargin cewa wani yunkuri ne na siyasa da gwamnatin PDP ta yi a jihar Bauchi.
Sannan ya yi Allah-wadai da zaben, inda ya ce, “Kamar yadda muka nuna a jiya, BASIEC ba ta da niyyar gudanar da sahihin zabe da gaskiya. Abin da muka shaida a yau a dukkan kananan hukumomi 20, wasan kwaikwayo ne na yaudara da izgili ga masu zabe da ’yan siyasa marasa laifi.”
“Zaben da ake kira zaben ya fuskanci kura-kurai da dama, da suka hada da rashin isassun kayan zabe, rike muhimman kayyayaki da takardar sakamako, kuri’un da aka ware wa PDP, rashin jami’an zabe da za su bayyana sakamako a hukumance, watsi da kayan zabe a rumfunan zabe da rashin gudanar da zabuka a mafi yawan rumfunan zabe a fadin jihar Bauchi.”
Jam’iyyar APC ta bukaci Ahmad Makama da ya yi murabus daga mukaminsa na Shugaban Hukumar cikin gaggawa, inda ta zarge shi da gaza aiwatar da rantsuwar da aka yi masa.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga BASIEC da ta soke zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 17 ga watan Agustan 2024 a jihar, inda ta bukaci gwamnatin jihar da ta rusa shugabancin hukumar zabe a halin yanzu tare da sake kafa tawaga mai inganci domin gudanar da sabon zabe wanda zai kasance cikin gaskiya da adalci, sahihanci, kuma daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya.
No comments