Daga Salisu Jibril Khidir Makarantar Zig-ziglar English Language Academy ta yi bikin yaye dalibanta a karo na farko. Bikin ya g...
Daga Salisu Jibril Khidir
Makarantar Zig-ziglar English Language Academy ta yi bikin yaye dalibanta a karo na farko.
Bikin ya gudana ne a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni, 2022 a harabar makarantar firamare na Dr. Justice Bashir Sabo da ke Lemu, Zariya. Wanda kuma ya sami halartar al'ummar daga sassa daban-daban na kasarnan.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron sun hada da Malam Muhammad Lawal Usman (Mai Elsa) Malami ga mai wannan makaranta, Malam Sani Umar Zig. Da Dr. Hamza Umar Assudany da sauran Manyan Malamai da dama. Wanda suma sun halarci wannan taro.
Taron ya sami karbuwa inda aka gabatar da jawabai tare da jan hankalin daliban da Kuma sauran al'umma da su dukufa da bincike. Yaye su bashi ke nuna sun kammala karatu ba, bil hasali yanzu aka fara.
An Kuma gargade su da su dukufa ka'in da na'in wajen binciken su. Yanzu sun sami shaidar koyar da harshen turanci a ko'ina a Nijeriya, ta hannun babban Malaminsu Malam Sani Umar (Zig Ziglar).
A karshe Malam Muhammad Mai Elsa ya yi kira ga al'umma da su daure su koyi wannan harshe na turanci. A cewarsa, "Wannan yare shi ne yaren kasa, kuma shi ne yaren da gwamnati ta ke magana da shi, shi ne yaren da ake a makarantunmu da wajen aikinmu da ma kusan duniya baki daya", inji shi.
Ya kuma yi kira ga matasa da su dage wajen neman ilimi domin ko shi ne mabudin arzikin duniya da ma lahira baki daya, kuma shi ne mu'ujizar Manzon Allah har a hura kaho babu wani abin alfahari sama da ilimi", ya tabbatar.
A karshe aka raba takardar shaidar kammalawa ga daliban da aka yaye, aka kuma dauki hotunan tarihi aka sallami kowa.
No comments