Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaban Majalisar Dattawa: Yadda Godswill Akpabio Ya Kada Abdul'aziz Yari

Sanata Godswill Akpabio ya yi nasarar zama Shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya ta goma, bayan zaɓaɓɓun 'yan majalisar datti...


Sanata Godswill Akpabio ya yi nasarar zama Shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya ta goma, bayan zaɓaɓɓun 'yan majalisar dattijai sun kaɗa ƙuri'a.

Akawun majalisar tarayya, Sani Tambuwal ne ya bayyana sakamakon zaɓen da 'yan majalisar suka yi, inda ya ce Sanata Godswill Akpabio ya yi nasara da rinjayen ƙuri'a 63.

Ya dai kayar da abokin fafatawarsa, Sanata Abdul'aziz Yari ne wanda ya samu ƙuri'a 46.

Tuni Akawu Sani Tambuwal ya rantsar da sabon Shugaban Majalisar Dattijan, bayan ƙuri'un da 'yan majalisa 107 suka kaɗa da safiyar Talata.

Matakin ya zo ne jim kaÉ—an da buÉ—e zaman majalisa ta goma a ranar Talata.

Magoya bayan sabon shugaban majalisar dattijan sun yi ta sowa a zauren majalisar inda suka je suna rungume Sanata Godswill Akpabio.

Da kammala zaÉ“en sabon shugaban majalisar dattijain kuma, yanzu an shiga matakin zaÉ“en mataimakinsa, inda Sanata Godswill Akpabio ya É—are kan kujerar shugaban majalisar dattijai. 

Sanata Nweze David Umahi ya gabatar da sunan Sanata Barau Jibrin a matsayin mutumin da yake son ganin an zaɓa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai ta goma.

Daga bisani, Sanata Salihu Mustapha ya goya masa baya a kan wannan buƙata.

No comments