Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wace Illa GB WhatsApp ke da shi? - Daga Ibraheem El-Tafseer

Wace illa manhajar GB WhatsApp ke da shi? Wannan ita ce tambayar da aka ta yi min a kwanan nan, sakamakon yadda mutane suke ta s...


Wace illa manhajar GB WhatsApp ke da shi? Wannan ita ce tambayar da aka ta yi min a kwanan nan, sakamakon yadda mutane suke ta sanarwa cewa, duk wanda yake amfani da GB Whatsapp ya gaggawar goge shi. 

Menene Illar GB WhatsApp?

Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana da wasu tsarurruka da 'Whatsapp' na asali ba shi da su, kamar irin su adana (saving) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga 'status(es)' na mutane kai tsaye, ko voye alamar karantawa ko karvar saqo, ko don yana nuna alamar in mutum yana online, ko don tura 'file' mai nauyi, ko voye groups/chats, ko rubuta sunan 'group' da harafai sama da 35, yin status da harufai 250, a taqaice. GBWhatsapp  yana da wasu ‘features’ da normal whatsapp ba shi da su.

Amma, yana da kyau mutum ya sani cewa duk waxannan tarko ne na masu kutse ko madatsa 'hackers'. Sun tsara shi ne ta yadda zai ba ka sha’awa sosai, fiye da manhajar WhatsApp na asali (normal Whatsapp), tare da ba ka damar wasan vuya da ma’abota amfani da normal Whatsapp, musamma ma mata. Ka tura saqo, a karanta, amma ba za ka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status xinka ba tare da ka ga wanda ya gani ba.

To dai maganar gaskiya, kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne, ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an qirqire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba. Ina shawartar masu amfani da GBWhatsapp, da masu sha'awar amfani da shi, da su qauracewa manhajar saboda waxannan dalilai; shi GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AlexMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya qa’idar qirqirar da ba da lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba za ka samu manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma tava ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.

Mai amfani da GBWhatsapp, ya sani cewa duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya leqawa ba, sayarwa, ko amfani da shi a duk lokacin da suka dama.

Idan aka turo ma wani saqo mai xauke da ‘virus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa 'spyware' ne. Duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi ya sa, yawancin waxanda ake musu kutse (hacking) na Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YOWhatsapp da sauransu.

GBWhatsapp ba ya restore (dawo da bayanai) a wasu lokutan, kamar yadda na faxa a sama, asali manhajar ta sava wa tsarin Google, kuma ana backup ne (yawanci) da Google account. Shi ya sa, da zarar ya yi 'expire' (wani lokaci) za ka rasa duk bayananka, har 'groups' da kake ciki, sai ka nemi a maida ka. Ka lura, a duk lokacin da ka xauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargaxeka cewa, wannan app xin zai iya cutar da kai, ko bayananka, ba ka tava lura ba ko? In ka tava lura da haka, don me za ka yarda?

Kai tsaye GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma a kowane lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin na har abada. 

Daga farkon watan nan dai zuwa yanzu, GB Whatsapp ya fara goge 'formatting' na wayoyin mutane. Sai ka buxe wayarka, sai ka ga an goge komai dake cikinta. Idan kana amfani da shi, ka yi gaggawwar cire shi, tun kan hakan ta faru da kai.

-eltafseerpen@gmail.com

No comments