Daga Ammar Muhammad Rajab Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan Nijeriya kan shirin gwamnatin taray...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan Nijeriya kan shirin gwamnatin tarayya da za ta bayyana nan ba da dadewa ba kan matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Yankin arewa maso yamma na fama da karuwar ‘yan bindiga wanda ya janyo asarar daruruwan rayuka tare da raba dubbai daga matsugunansu inda tuni masu ruwa da tsaki a kan harkokin tsaro da dama ke ba da shawarar wata hanya ta daban wacce ba ta karfin soja kadai ba.
Sai dai rahotanni sun ce babban hafsan sojin kasar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya yi kaca-kaca da shirin yin afuwa ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kasar a makon jiya, inda ya ce maimakon su tuba, masu cin gajiyar irin wadannan shirye-shiryen na kallon shirin a matsayin wata hanya ta sake haduwa da shirya kansu domin kai hari ga ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Sai dai da yake magana a Kano ranar Lahadi, mataimakin shugaban kasar ya ce shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kuduri aniyar sake fayyace ma’ana dangane da tsarin mulkin zamani.
Ya ce ba za a dogara kadai da hanyar soji ba domin magance rikicin yankin Arewa maso Yamma ba.
Ya ce, “Rikicin da muke fama da shi a yankin Arewa maso Yamma, wanda talauci da wariyar al’umma ke kara ta’azzara shi, abu ne da shugaban kasa ya kuduri aniyar tunkararsa a gaba kuma nan da makonni masu zuwa, zai kaddamar da mafita.
Ya kara da cewa; “Sai dai idan muna so mu shiga yakin basasa mara iyaka, ba za a dogara da hanyar soji kadai ba wajen magance rikicin Arewa maso Yamma ba. Dole ne a samar da hanyoyin kwantar da tarzoma ba tare da tashin hankali ba. Kuma Shugaba Bola Tinubu nan da makonni biyu masu zuwa zai kaddamar da shirin Pulaku wanda zai magance korafe-korafe da rashin jin dadin rayuwar ‘yan'uwanmu na Fulbe a Arewa maso Yamma; don magance tushen duk wata ta'addanci da tada kayar baya a cikin al'umma."
No comments