Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Alhamis, ya karrama mahajacciyar da ta mayar da dala 80,000 da ta tsinta ga mai shi a aikin Ha...
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Alhamis, ya karrama mahajacciyar da ta mayar da dala 80,000 da ta tsinta ga mai shi a aikin Hajjin da ya gabata a kasar Saudiyya.
Mahajjaciyar,
Hajiya Aishatu 'yan Guru Nahuce daga karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara
ta tsinci dala 80,000 kwatankwacin naira miliyan sittin da hudu da dubu dari
biyu da arba’in (N64,240,000) sannan ta mika wadannan makudan kudaden ga
jami'in hukumar jin dadin alhazai ta Zamfara domin ganin an mayar da kudaden ga
mai shi.
A
wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya
fitar, ya ce gwamnan ya karrama mahajacciyar ne a gaban dukkanin Sarakunan
jihar a zauren majalisa da ke gidan gwamnati.
Gwamnan
ya kuma bayyana matukar farin cikin gwamnatin jihar bisa gaskiyar da wannan
mahajjacciya ta nuna.
“Dukkan
al’ummar jihar Zamfara suna alfahari da farin ciki kan abin da Hajiya A’ishatu
ta yi a Saudiyya. Ya kara wa daukacin al’ummar Zamfara suna.
“Wannan
abin alfahari ne a gare mu ba kawai ga Hajiya A’isha ba, ta rubuta sunanta a
cikin litattafan tarihi masu kyau. Irin wannan aiki abin so ne ga duk wani
Musulmi mai imani, musamman ma a kasa mai tsarki.
“Mun
ga misalin aikin kwarai na gaskiya da ya kamata a yi koyi da shi daga Hajiya
A’isha, ki yarda da ni, ba kowa ne zai iya tsintar irin wadannan makudan kudade
a wurin da ba kowa, kuma ya mayar da su.
“Gwamnatin
jihar Zamfara za ta yi duk abin da yakamata wajen taimakawa iyalan Hajiya
Aisha.
“Shugaba
Bola Ahmed Tinubu shima zai karrama Hajiya A'isha bisa wannan kyakkyawan aiki
na gaskiya.”
Tun
da farko, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin gabatar da Hajiya
A’isha, ya jaddada cewa matakin da ta dauka ya kara mutunta al’ummar Zamfara
baki daya.
Hajiya
Aisha ita ma ta yi bayanin yadda lamarin ya faru a kasa mai tsarki a Saudiyya.
No comments