Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hazikin Matashi: Yadda Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Ya Kafa Jami’o’i Hudu a Cikin shekara 10

*Ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Maradi yana da shekaru ashirin da tara a duniya Daga Ammar Muhammad Raj...

*Ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Maradi yana da shekaru ashirin da tara a duniya

Daga Ammar Muhammad Rajab

Shin kun taba ji ko gani ko karanta labarin matashin da ya kafa jami’a yana da shekaru 29? Kun taba jin labarin wanda ya kafa jami’o’i hudu cikin shekaru 10 a tsakanin kasashe biyu? Jaridar MADOGARA ta yi nazarin yadda Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya kafa jami’o’i hudu ringis cikin shekaru 10 a tsakanin Nijeriya da jamhuriyyar kasar Nijer.

Saboda aikata alherinsa ga mabukata, yana da wuya a duniyarmu ta yau ga mai bibiyar harkokin yau da kullum ya zama bai taba jin sunan Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ba. Saboda irin gudummawar da yake bai wa harkokin ilimi da al’umma a Nijeriya da ma Afrika baki daya da kuma jin kai da yake nuna wa a koyaushe.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya dauki bangaren ilimi da muhimmanci; domin ya fahimci cewa da ilimi ne kawai za a iya ‘yantar da al’ummar duniya, wannan dalilin da ma saura, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya zuba dimbin hannun jari ba don riba ba wajen ganin al’umma sun samu ingantacce kuma nagartaccen ilmi da za a yi gogayya da su a duniya wajen bai wa marada kunya.

Farfesa Adamu gwarzo, hazikin matashi, ya zama ginshiki ga ilimin zamani a Nijeriya da ma Afrika baki daya. Domin mutum ne da ya bada himma wajen samar da tsarin ilimi wanda duniya ke da bukata a yau.

Farfesa Gwarzo mutum ne da ya yarda da koyon harsuna fiye da daya domin tafiya da duniya ta yadda duk wata dama idan ta zo, mutum ka iya samun sa a duk bangaren ilimin da kake.

A cikin hirarsa da BBC Hausa, ya ce burinsa shi ne ilmantar da mutum miliyan ɗaya kafin ya bar duniya. Bayanai da jaridar MADOGARA ta samu na nuni cewa; ya zuwa yanzu daruruwan dalibai ne Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bai wa ilimi kyauta a jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer. Wannan tallafin karatu kyauta ya bayar ga masu kudi da kuma talaka domin bunkasa ilimin ‘ya’ya masu tasowa.

Bayanai sun nuna cewa; an haifi Farfesa Gwarzo a shekarun saba’i’noni, a Anguwar Agege dake garin Legas.  Sai dai asalin mahaifinsa ya fito ne daga Sabon Layin Kara dake garin Gwarzo a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano. Saboda kishinsa da Arewa da al’ummar karamar hukumar Gwarzo ya sa bai alakanta kansa da Legas ko Agege ba, yake kiran kansa da Adamu Abubakar Gwarzo. Ya sami digirinsa na farko a harshen Faransanci, haka ma digirinsa na biyu da digirin digirgir wato PhD.  Sannan ya yi wani PhD din a bangaren ‘Higher Education’ duk a kasar Faransa.

Yana da shaidar zama Farfesa a bangare biyu na ilimi da ya hada; Farfesa a Harsunan zamani na Turai sannan kuma Farfesa a ne a bangaren shugabanci.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo fitaccen Malami ne a Nijeriya kuma fitaccen mai ayyukan jin kai ne wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen bunkasa ilimi da al’umma a Nijeriya da Afirka da duniya baki daya. Farfesa Gwarzo yana da kwarewa a bangaren harkokin kasuwanci, mutuntaka, harkokin ilimi. Sannan gogaggen dan jarida ne da ya kwashe shekaru yana aiki. Sannan ya rike shugabancin kungiyar kare hakkin ‘yan jarida na Afrika.

A takaice Farfesa Gwarzo Malami ne, dan jarida ne, dan kasuwa ne, mai bincike ne, babban manaja ne, sannan jagora ne a bangaren ilimin jami’a.

Ya kafa jami’arsa ta farko yana da shekaru 29 a duniya a shekarar 2013. Ya kafa jami’ar ne a garin Maradi ta jamhuriyyar kasar Nijer. Inda ta kasance jami’a ta farko a kasar Nijer wacce take koyarwa da harshen ingilishi. Sannan jami’ar ta kasance ta farko da ake kwarewa a harsuna biyu na Faransanci da turanci. Sunan Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) Maradi.

Bayan kamar shekaru 10 da kafa Jami’ar MAAUN dake Nijer, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya kafa wata jami’ar irinta a Kano da aka sanya wa suna Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) Kano. Inda a tashin farko jami’ar ta soma karatu da daruruwan dalibai a zangon karatu na 2021/2022.

A cikin watan Yunin 2023 ne, hukumar lura da jami’o’in Nijeriya ta sake bai wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo lasisin kafa jami’o’i guda biyu da suka hada da; Franco British International University a Kaduna da kuma Canadian University na Nijeriya a birnin Tarayya Abuja.

A ranar 12 ga watan Yulin 2023 kwamitin amintattu na Jami’ar Franco-British International University dake Kaduna, ta amince da naɗin Farfesa Abdullahi Muhammad Sabo a matsayin mataimakin shugaban sabuwar jami’ar.

Wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya sanar da naɗin a lokacin da yake miƙa takardar naɗin ga Farfesa Sabo a ranar Laraba, 12 ga Yuli, 2023.

Saboda irin gudummawar da yake bai wa harkar ilimi, ya sanya jami’ar IHERIS dake kasar Togo ta nada shi a matsayin Pro-Chancellor na jami’ar. Wanda har ya zuwa hada rahoton nan shi ne ke rike da wannan mukamin.

Dangane da irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa a fannin ilimi da al’umma, Farfesa Gwarzo ya samu kyautuka da yawa daga jami'o'i, dalibai, hukumomin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, abokan huldar ci gaba, da sauran al'ummomi a fadin duniya.

Yana rike da kambun “Sarkin Yaki Da Jahilci na Afrika” wanda hukumar al'adu ta Nijar tare da hadin gwiwar kungiyoyi suka ba shi. A cikin shekarnan ta 2023, aka ba shi lambar yabo a matsayin Jagora mai fasaha da kirkira wanda ‘World Education’ da ‘EDTech 2nd’ suka ba shi a New Delhi, dake Indiya.

Farfesa Gwarzo bai tsaya a bangaren ilimi kadai ba, yana bayar da gudummawa a fannoni daban-daban. Yana bada gudunmawarsa mara yankewa. Gidauniyarsa ta ‘Adamu Abubakar Gwarzo Foundation’ ta zama jigo wajen share hawayen dubban al’umma. Gidauniyar na kashe miliyoyin kudade domin biyan bukatun al’umma. Taimakon da yake bayarwa a karkashin wannan gidauniyyah ba kawai ga ‘yan Nijeriya kadai bane harma da wasu kasashen Afrika.

A shekarar 2021, Gidauniyar Adamu Gwarzo ta ba da gudummawar mota kirar bas mai cin mutane 66 na alfarma wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 50 da kuma motar daukar marasa lafiya ta Naira miliyan 20 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano Wudil (KUST). Haka kuma gidauniyar ta bayar da kyautar mota kirar bas mai cin mutane 60 ga Kaduna Polytechnic, haka zalika, gidauniyar ta bayar da kyautar motar alfarma mai kujeru 66 da kudinta ya kai Naira miliyan 50 ga jami’ar Al-Istiqama dake Sumaila ta jihar Kano. Sannan gidauniyar ta Gwarzo ta bayar da tallafin motocin bas masu kujeru 60 na Mercedes-Benz ga jami’ar Bayero da ke Kano da kuma jami’ar gwamnatin Nijar.

Gidauniyyar har wala yau ta tallafa da kudi har naira miliyun biyu wajen buga littattafai guda biyu. Littafan sune; “Pantami: The Trials and Triumphs of a Digital Economy Maestro,” na Mal. Yushau Shuaib da kuma “eNaira Revolution: A Peep into Nigeria’s Cashless Future,” wanda Mista Abdulrahman Abdulraheem ya rubuta. A shekarar 2022, Gidauniyar Gwarzo ta bai wa mata marasa karfi 100 na jihar Kano tallafin naira dubu hamsin (N50,000) ga kowaccensu. A shekarar 2022, Gidauniyar Gwarzo ta ba da tallafin Naira Miliyan 1 ga dalibin Nijeriya da yake karantar fannin likitanci da ya makale a kasar Rasha.

Sannan har wala yau gidauniyyar Adamu Abubakar Gwarzo a kokarinta na magance matsalar ruwan sha a wurare daban-daban ta gina rijiyoyin burtsatsai kyauta har guda 100 a garuruwa daban-daban lungu da sakon na karamar hukumar Gwarzo.

Za a iya cewa; Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya kafa tubalin samun nagartaccen ilimi da bunkasa rayuwar al’umma a Afrika baki daya. Sannan ya kafa gidauniyyar share hawayen al’umma wanda za ta ci gaba da amfana har a nade kasa. Sannan da wannan ya cancanci kambun ‘JAKADAN SAMUN INGANTACCEN ILIMI NA AFRIKA’. Wannan kambu ne da Jaridar MADOGARA ta ba shi. 

No comments