Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE
Thursday, June 26

Pages

Labarai:

'Yan shi'a sun yi muzaharar Ashura a Zariya

*Makasudin fitowarmu –Shaikh Abdulhamid Bello Daga Zailani Mustapha ‘Yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky kamar yad...


*Makasudin fitowarmu –Shaikh Abdulhamid Bello

Daga Zailani Mustapha

‘Yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky kamar yadda suka saba a duk shekara sun gudanar da muzaharar Ashura a garin Zariya ta jihar Kaduna. Wakilinmu ya labarto cewa; muzaharar ta gudana ne da safiyar yau Juma’a 10 ga Al-Muharram 1445 daidai da 28 ga Yulin 2023. An soma da misalin karfe 8 na safe sannan aka kammala wajen karfe 12 na rana.

Muzaharar ta taso ne daga Kofar Doka, inda aka rufe a Gwargwaje duk a cikin garin Zariya.

Masu muzaharar wanda ya hada maza da mata, yara da manya, matasa da tsofaffi sun kasance cikin sahu-sahu bisa tsari sanye da bakin kaya suna tafe suna rera wakokin alhini da juyayi na kisan gillar da aka yi wa jikan Manzon Allah (SAWW), Imam Hussaini da iyalan gidansa da Sahabbansa a filin Karbala a shekara ta 61 bayan hijirar Manzon Allah (S).

Masu muzaharar har wala yau suna tafe dauke da tutoci da fastoci da ke alamta juyayi da isar da sako ga wannan al’umma. Sannan akwai masu wasan kwaikwayo dake alamta abin da ya faru a Karbala bayan kashe jikan Manzon Allah, Imam Husaini.

Shaikh Abdulhamid Bello shi ne wakilin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a garin na Zariya, a yayin jawabin rufewa ya bayyana cewa; “muna godiya ga Allah ta’ala da ya nufe mu da soma wannan muzahara lafiya ga shi har an zo inda za a kammala lafiya”, ya lurantar.

Da yake bayyana makasudin fitowarsu, Shehin Malamin ya ce; “kamar yadda aka sani wannan muzahara ta tunawa ce da shahadar Abi Abdullahil Husain (A.S), wanda ya kasance a daidai lokaci irin wannan rana ta 10 ga watan Al-Muharram shekara ta 61 bayan hijira. Mun fito ne cikin bakaken kaya muna zubda hawaye muna juyayi, muna jimami da bakin ciki da tunawa da wannan waki’ar da ta faru. Wannan bangaren adifa ke nan. A lokaci guda kuma muna isar da sako ga wannan al’umma da take raye a yanzu saboda mun samu kanmu a irin yanayin da Imam Husain (AS) ya samu kansa a wancan zamani”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “inda yanayin al’amura suka tabarbare, mutane sun bar biyayya ga Allah (SWT), sun koma sun zama ma’abota duniya ne kawai. Wanda ya sa Imam Husaini ya fito domin ya samar da gyara da sauyi a cikin al’umma. Wannan gyara muna matukar bukatarsa a irin wannan zamani da muka samu kanmu a ciki”, ya nusantar.

Shaikh Abdulhamid Bello a wani bangare na jawabinsa har wala yau ya ce irin takala da makiya a yau suke yi wa Musulunci akwai bukatar al’ummar Musulmi su farka su kawo gyara; “wanda ya zama a yau ba kawai tunawa da bakin cikin abin da ya faru a Ashura ba, harma tunawa da takalar da al’ummar yau suke yi wa alamomin addini kamar yadda ake kona Alkur’ani a kasashen kafirai. Kamar yadda aka yi a Sweden ba sau daya ba ba sau biyu ba. Da ainihin batanci ga ma’aiki (SAWW)”, in ji shi.

Ya kuma ce; “Duk wadannan wasu abubuwa ne da suke nuna cewa mu al’ummar Musulmi suna ganin ko mun mutu ne ko muna bacci ne ya sa ake yi mana wannan, to wajibi ne mu farka. Mu san cewa hakkinmu ne mu kare alamomin addini. Kuma tabbatar addini ya mamaye duniya, dole ne sai mun dauki irin matakin da Imam Husaini ya dauka na sadaukarwa da cire tsoro a zukatanmu da cire biyayya ga mutanen da duniya kawai suka sa wa gaba. Da wannan za mu samu nasara!”, ya tabbatar.

“yakamata mu farka mu kwato ‘yancinmu da al’amuranmu baki daya, al’amura su gyaru su daidaitu. Ba ranar da wadannan azzalumai za su sallama mana su ce mu yi addini. Addini kwato shi ake yi da karfi. Dole ne mu sani cewa mu fadakar da juna mu sadaukar mu kwato ‘yancinmu daga hannun wadannan azzalumai”, ya jaddada.

Ya nusasshe da cewa; Ashura yana firgitar da azzalumai. Bayan kammala jawabinsa, an yi addu’a aka sallami mutane.

Wakilinmu da ya kasance tun daga farkon muzaharar har karshe ya labarto mana cewa; an yi muzaharar lafiya an kuma kammala lafiya.

No comments