Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal tare da sauran gwamnonin Nijeriya sun halarci taron majalisar tattalin arzikin ƙasa yau, a fa...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal tare da sauran gwamnonin Nijeriya sun halarci taron majalisar tattalin arzikin ƙasa yau, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Hakan na kunshe ne a sanarwar da Sulaiman Bala Idris, Babban Mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai ga Gwamnan jihar Zamfara ya fitar a ranar Alhamis.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci zaman, inda aka tattauna muhimman batutuwa na tattalin arziki, musamman hanyoyin samar da sauƙi ga jama'a a wannan halin da ake ciki na hauhawar farashin man fetur.
No comments