Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo Ya Kai Ziyarar Ta’aziyyah Ga Shugaban Kamfanin Max Air, Dahiru Mangal A Katsina

    A ranar Alhamis 20 ga watan Yuli, 2023, Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Far...

 


 A ranar Alhamis 20 ga watan Yuli, 2023, Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jagoranci wasu jami’an gudanarwa na Jami’ar zuwa Katsina domin ziyarar ta’aziyya ga Shugaban Kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Barau Mangal bisa rasuwar matarsa, Hajiya A’isha Mangal.

Hajiya A’isha ta rasu ne a ranar Asabar, 15 ga Yuli, 2023, a wani asibiti da ke Abuja bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Daga cikin ma’aikatan gudanarwar da suka raka Farfesa Gwarzo a ziyarar sun hada da Shugaban Jami’ar, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, mataimakin Shugaba bangaren gudanarwa, Dakta Habib Awais Abubakar, da mataimakin shugaban jami’ar MAAUN-Maradi, Nijar bangaren gudanarwa. Dr. Shu’aibu Usman Tanko.

Sauran sun hada da mataimakin Shugaban Jami’ar Franco-British International University, Kaduna, Farfesa Abdullahi Muhammad Sabo, Daraktan hadin gwiwa da kulla alaka, Dakta Bala Muhammad Tukur, sai Dakta Lawal Kankia, Shugaban Tsangayar aikin jarida na jami’ar MAAUN- Maradi, da Dakta Bala Zango da kuma Shugaban Ofishin huldar kasa da kasa, Injiniya Bashir Garba, da sauransu.

Yayin da yake jajantawa hamshakin dan kasuwar na Katsina, Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar jami’o’i masu zaman kansu na Afrika (AAPU), ya bayyana rasuwar Hajiya A’isha a matsayin babban rashi ba kawai ga danginta kadai ba, har ma da daukacin al’ummar jihar Katsina.

“Zuciyarmu ta yi nauyi bisa samun labarin rasuwar masoyiyar matarka Hajiya Aisha ba zato ba tsammani.

“A madadin iyalaina da kuma Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da Nijer, muna mika sakon ta’aziyyarmu zuwa gare ku bisa rasuwarta ba zato ba tsammani.

“Ina son na kuma yi amfani da wannan damar domin jajanta wa daukacin iyalan marigayiyar bisa wannan babban rashi da aka yi. Allah madaukakin Sarki ya bai wa daukacin iyali ikon jure wannan rashin da ba za a iya mayarwa ba,” in ji Farfesa Gwarzo.

Sannan ya roki Allah madaukakin Sarki da ya gafarta mata kurakuranta, ya shigar da ita a Jannatul Firdausi.

A yayin ziyarar ta'aziyyar an gudanar da addu'a ta musamman ga mamaciyar inda aka karanta wasu ayoyin kur'ani mai tsarki.

 

Marigayi Hajiya A’isha Mangal ta rasu ta bar mijinta, ‘ya’yanta, da kuma jikoki, kuma tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Katsina.

Allah ya jikanta da Rahama, yasa ta huta, amin.

No comments