Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DPO Ya Biyawa Saurayin Da Ya Gaza Biyan Sadaki A Kaduna

Daga Hussaini Yero Masu iya magana na cewa, na Allah ba ya karewa, musamman ba a cika yi wa 'yan Sanda zaton alkhairi ba, sa...


Daga Hussaini Yero

Masu iya magana na cewa, na Allah ba ya karewa, musamman ba a cika yi wa 'yan Sanda zaton alkhairi ba, sai gashi DPO na Millonia City Kaduna, Lawal Abdullah ya biya sadakin saurayin da aka kai kararsa wajen shi dan ya gaza biyan sadakin dubu ashirin da aka sa masa, a nan take DPO Lawal Abdullah ya biya wa saurayin Aliyu sadakin dubu hamsin da uku.

Masarautar Dan Bushiya da ke cikin Kaduna ne ta kai karar Saurayin ga DPO don ya yi amfani da karfin Damaransa wajen raba Aliyu da Buduwarsa Maryam wace aka sa masa sadakin dubu ashirin ya gaza biya wata da watanni .

Kuma saurayin ya ki rabuwa da buduwar ta sa shi me Sarkin Dan Bushiya da ke jagorantar hidimar ya kai kara Aliyu wajen DPO din ya raba su da ita, sai gashi a nan take DPO Lawal Abdullah ya zare kudin har dubu hamsin da uku kamar yadda shari'a ta ce a biya wa saurayin Sadaki aka daura auren a nan take.

Sakataren Sarki Umar Yakubu ya jinjinwa DPO Lawal Abdullah a bisa kokarin da ya yi na ceto Maryam daga halin da take ciki donin marainiya ce shi kuma Aliyu Iyayen sa ba su da karfin yi masa aure.

Sakataren Sarki ya bayyana cewa,ya kwashe sheru 40 na Sakataren Sarki bai taba ganin ma'aikacin Damara ba mai tausayi irin DPO Lawal Abdullah ba. A cewarsa abunda muka yi tsammani shin
 ne Aliyu ya gamu da hukunci mai tsauri don ya rabu da Maryam ta samu wani ta aura sai gashi reshe ya juye da mujiya Maryam ta zama matarsa gidan 'Yan Sanda.

Akan haka ne Umar Yakubu ya yi kira ga hukumar rundudar 'Yan Sanda da su karawa DPO Lawal Abdullah mukami da lanbar yabo wajan sasanta alumma dan samun cikaken zaman lafiya .
Sakataren yayi kira ga 'Yan Sanda da suyi koyi da DPO Lawal Abdullah wajen aiki na gari da sulhunta Jama'a ba tare da anje kotu ba .

No comments