Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Samar Da Tsari Don Inganta Karatun Almajiranci - Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman

Daga Hassan Ibrahim Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani kan...


Daga Hassan Ibrahim

Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani kan harkokin addini ya jaddada manufa da ƙudirin Gwamnatin na samar da tsare-tsare don inganta walwala da jin dadin al'ummar jihar.

Ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya karɓi lambar karramawa daga Ƙungiyar Mawallafan Jaridu ta Arewacin Nijeriya (Arewa Publishers Forum), dake da babban ofishinta a jihar Sakkwato.

Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman ya ce cikin tsare-tsare da gwamnatin za ta yi shi ne inganta tsarin al’majiranci domin samun ingantaccen ci gaban da ake bukata wajen gina al’umma, domin za mu mayar da komai ya zamo daidai da zamani a samu ingantaccen ilimi domin ci gaban al'umma baki É—aya, in ji shi. 

Babban mataimakin ga Gwamnan Jihar Kaduna, Abdulrahman Zakariyya Usman, ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta sanya batun zaman lafiya da haɗin kan juna ne musamman ga ƙungiyoyin addini ta sanya a gaba.

“Ina tabbatarwa kowa da cewa Gwamnatin Uba Sani ta hanyar ofishina na mai bashi shawara a kan harkokin addinin Musulunci za mu yi tafiya da kowace Æ™ungiyar addini har waÉ—anda ma ba su da wani addini ba tare da wani bambanci ba.

“Ba Gwamnatin da za ta zura idanu kawai ta na kallon al’umma ba tare da yin abin da zai ciyar da su gaba ba, hakan ya sa Gwamantin Uba Sani na da cikakken sani da shirin da za ta dubi wannan harka sosai da nufin a samu ci gaba dangane da wannan hanya ta Almajiranci domin hanya ce ta Koyar da karatun Alkur’ani kuma hanya ce da duk wani gyara da garambawul da ake nufi lallai za a samar da shi cikin hukuncin Allah ba tare da an tsangwami kowa ba ko sanya jama’a a cikin wata damuwa ba”.

Kazalika,ya kuma yi kira ga sauran mabiya addinai da cewa haÆ™iÆ™a Gwamnatin Malam Uba Sani gwamnati ce da ke neman haÉ—in kan al’umma domin babu gwamnatin da za ta ci gaba idan al’ummarta ba su haÉ—a kai ba.

“Domin babu wanda zai kawo hannun jari ko duk wata dukiyarsa idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda haka ne wannan Gwannatin a duk tsakanin Æ™ungiyoyi babu abin da take fata da ya wuce haÉ—in kai da tunanin yadda za a ciyar da Æ™asa gaba a kuma yada batun zaman lafiya a tsakanin al’umma, wannan shi ne babban fata na mai girma Gwamna da Gwamnatinsa mai albarka da yardar Allah”.

No comments