Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JUYIN MULKI A JAMHURIYAR NIJER: Binciken Masana Game Da Mulkin Malam Bazoum Muhammad

Jiya Laraba da misalin karfe Biyar zuwa Shidda na safiya aka fara jin rade raden cewa an yi wa Shugaban Kasa Malam Muhammad Bazoum Juyin Mul...

Jiya Laraba da misalin karfe Biyar zuwa Shidda na safiya aka fara jin rade raden cewa an yi wa Shugaban Kasa Malam Muhammad Bazoum Juyin Mulki lamarin da ya jefa Kasar da Al'ummar cikin wani irin yanayin marar dadi tare da tambayar kansu ko minene dalili ko makasudin kokarin kifar da Gwamnatin a lokacin da take shekara biyu da Wata Biyar Da hawa karagar mulki.

Bazoum Muhammad yana da wani salon mulkin da ba kowa yake da irin irinshi ba, duba da cewa mafi yawan Shugabannin Kasashe suna sauye sauye ko nade naden a lokacin da suka karbi karagar Mulki, maimakon hakan shugaba Bazoum din ya cigaba da tafiya da shugaban sojojin mai kula da Fadar Shugaba Kasa mai suna General Abdurahaman Tchani wanda ya kwashe kusan shekara goma tare da tsohon shugaban kasa Muhammadu Issoufou daga bisani ya cigaba da tafiya da Bazoum bayan saukar Magajin nashi.

Dayawa masana Siyasa na ganin sakaci da halin ko in kula na Shugaba Bazoum saboda rashin kawo sauye sauye ga shugaban, sannan suna nuna cewa wannan shi ne babban kuskuren da ya yi da har aka kawo wannan matakin na juyin Mulki, yayin da wasu kuma ke ganin cewa akwai hadin bakin tsohon shugaban kasa Muhammadu Issoufou saboda General Abdurahaman Tchani yaronsa ne kuma shi ya saka Bazoum ya barshi maimakon ya chanza ya saka nashi

Tun bayan jin labarin Juyin Mulkin wasu magoyan Malam Bazoum sun fito a manyan titunan babban Birnin Niamey domin rashin goyon bayansu ga Juyin Mulkin, Jami'an tsaro sojojin suka mayar da su cikin lokacin, a wata majiyarma har sun amfani da karfin Bindiga. 

Tun da yammacin jiya al'umma suke da kokarin jin halin da ake ciki ta hanyar manyan Gidajen Radio fara daga BBC Hausa, DW Hausa, Rediyo France, da TRT Hausa, da sauran manyan kafafen yada na zamani, inda daga karshe misalin sha biyu na Dare (RTN) Radio Television Niger suka tabbatar da Juyin Mulkin ya tabbata tare da saka hutan wasu daga cikin manyan Sojojin da suka jagoranci juyin mulkin. 

Haka kuma wasu daga cikin Masana siyasar Duniya na cewa Kasar Faransa na da hannu dubu dubu wajen aiwatar da Juyin Mulki saboda Bazoum ya aiwatar da abubuwa dayawa na kin kasar ta Faransa fara daga sauya Tutar Kasar da ya yi da kuma kudurinsa na sauya kudin wanda suke ganin yana kokarin yi masu turjiya ko ballewa daga tsarin na Faransa. 

A safiyar Yau Ministan harkokin wajen Kasar Hassimi Masa'udu ya yi wa Radio France Africa karin bayani akan cewa har yanzu suna cikin tattaunawa kan batun na Juyin Mulki, saboda tun jiya wasu Jaridun Kasar sun bada labarin cewa Shugaban ECOWAS President Bola Ahmed Tinubu ya aiko da wakilai, tare da Shugaban Kasar Benin Patrice Talon domin su sassanta. 

Sannan kuma mafi yawan masana siyasa na ganin Bazoum a matsayin dan siyasar marar gaba, kusan shekara biyu da wata hudu babu abunda Shugaban yake yi illa kokarin sasantawa tare da jawo abokan gaba domin su yi tafiya tare, wannan yana daga cikin dalilin da wasu ke kallon shi a matsayin mai saukin kai ko marar gaba. 

Har yanzu da nake rubuta wannan rahoto babu takamaiman wanda aka sanar a matsayin shugaba ko ya jagoranci juyin mulkin kasar, daga karshe ana ta rade radin cewa an. Kama tsohon shugaban kasa Muhammad Issoufou, shi kuma Bazoum din wata majiyar na cewa shi da iyalinshi suna cikin koshin lafiya a hannun jami’an tsaron na Soja. 

Zahraddeen Sirajo Abbas 

Dan Jarida Mai Bincike 

Zahradeensirajoabbas@gmail.com

No comments