Gwamna Dauda Lawal, a ranar Laraba, ya karbi rahoton wucin gadi daga kwamitin ba da shawara kan farfado da ruwan sha na jihar Zamfara, yan...
Gwamna Dauda Lawal, a ranar Laraba, ya karbi rahoton wucin gadi daga kwamitin ba da shawara kan farfado da ruwan sha na jihar Zamfara, yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na samar wa da babban birnin jihar da sauran kananan hukumomin jihar da tsaftataccen ruwa, wadatacce kuma mai dorewa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa gwamna Lawal ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake karbar rahoton a zauren majalisar da ke gidan gwamnati da ke Gusau.
Gwamnan ya yabawa tawagar bisa hidimar da suke yi wa jihar da kuma bayar da gudunmawar su wajen ciyar da manufar gwamnati ta magance matsalar karancin ruwan sha a fadin jihar Zamfara.
“Abin farin ciki ne a gare mu da muka samu wannan rahoton na wucin gadi, la’akari da cewa jiharmu na fuskantar matsalar karancin ruwa. Wannan yana daga cikin ginshiÆ™an Æ™udirinmu na rage radadin da al'umma ke ciki, kuma ba shakka, tare da samar musu da ruwan sha.
“Na yi alkawurra a lokacin yakin neman zabe wanda daga ciki ya hada da magance matsalar rashin ruwa. Ina so in tabbatar wa nagartattun al’ummar Zamfara cewa gwamnatina za ta yi duk abin da za ta yi na jin kai domin magance wannan matsala.
"Na yi imani cewa da wannan kwamiti, za mu cimma nasara insha Allah. Za duba rahoton kuma mu yi nazarinsa sosai a tsanaki. Za mu yi la'akari da shawarwarin da ke ciki sannan mu yi abin da ya dace domin magance matsalar da ya ki ci ya ki cinyewa.
“Bugu da kari kuma, ina mai farin cikin ganin yadda kwamitin zai fadada ayyukansa zuwa sauran kananan hukumomin, wanda zai samarwa da daukacin al’ummar Zamfara wadataccen ruwan sha. Ina so in gode wa ’yan kwamitin da suka yi wannan gagarumin aiki, jajircewar ku abin yabawa ne.”
Tun da farko shugaban kwamitin Injiniya Bawa Sani Dauran ya yi bayani dalla-dalla kan yadda kwamitin ba da shawarar kan farfado da ruwan sha ya gudanar da aikinsa.
No comments