Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Neman Yafiyar Waɗanda Mu Ka Yi Wa Ba Daidai Ba, Shugaban 'yan kasuwar Sabon Gari, Ibrahim Mai Gwal

  Daga Hassan Ibrahim Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwan Sabon Garin Zariya na jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim mai Gwal, ya buƙaci ƴan kasuwan wajen...

 


Daga Hassan Ibrahim

Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwan Sabon Garin Zariya na jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim mai Gwal, ya buƙaci ƴan kasuwan wajen yafe masa bisa laifin da ya yi musu lokacin gudanar da jogarancin kasuwan tsawon shekarun da ya yi yana gudanar da mulkinsa.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƴan takarar kasuwan, ƙarƙashin jagorancin mai neman shugabancin ƙungiyar ƴan kasuwan, Alhaji Abbas Tanko (Sardauna) a kasuwar Sabon Garin, Zariya.

Alhaji Ibrahim Mai Gwal ya bayyana cewa cikin lokacin jagorancin kasuwan,ya samar da tsare-tsare don jin daɗin 'yan kasuwan da kuma cigaban kasuwan baki daya.

Ya ce yana amfani da wannan dama wajen neman yafiyar al'ummar kasuwan wanda ya saba musu bisa kuskure.

"Dan Adam ajizi ne, zaka iya saɓawa wani bisa kuskure,wanda muka saɓa musu, su yafe mana,wanda kuma muka yi ma daidai, mun gode", in ji shi. 

Ya nuna jin daɗinsa bisa irin goyon bayan da ƴan kasuwan suka bawa ɗan takarar, kuma yana yi wa kowa fatan alkhairi da irin wannan karamci da aka yi musu.

Ya ce wannan tafiya da aka fara tafiya ce mai haske wanda aka yi ta tsawon shekaru takwas, kuma  Sardauna shi ke takara ba mai Gwal ba. Yana mai cewa, ranar da za a fara kamfen ranar ne zamu fito don nuna muku muna neman goyon bayan ku.

Kazalika,ya yi nuni da cewa,ƴan kasuwa su sani maganar rushe kasuwa da ake zargin mu da shi, kasuwanni goma 16 aka rusa a jihar Kaduna, kuma ba mai Gwal bane ya nemi haka ba, bai isa ya ce Gwamna ya gina mai shago ba.

Ya ce kasuwanni 16 da aka fara ginawa an yi  musu alƙawarin kashi 10 kuma banda  kasuwan Sabon Garin Zariya, ba wanda aka fara ba wa kuɗin, wanda yanzu an bada runfuna 330 kuma gwamnar jihar Kaduna ƙarƙashin Sanata Uba Sani ya tabbatar masu da cewa, bayan sun gama raba madafun iko duk wanda ya buƙaci kashi 10 za a bashi da yardar Allah.

Abbas A. Tanko wanda aka fi sani da Sardauna, mataimakin shugaban ƴan kasuwan Sabon Gari, (Vice ll) kuma ɗan takarar shugabancin kasuwar Sabon Gari, ya ce duba da haɗin kan da al'umma suka bayar na nuni da cewa a nan zaman lafiya da al'ummar kasuwar.

A cewar shi,muna sane da irin tsare tsare da gwamnati mai ci ta yi musu kuma suna kanta, a don haka suke bada goyon bayan da alƙawarin inda aka tsaya za a cigaba, inda aka yi kuskure kuma za a gyara.

A don haka, yake kira ga al'ummar kasuwar Sabon Gari da su san da cewa, cikin masu neman takara su auna kowanne akan sikeli, me ya yi a baya kuma mene ne tsare-tsaren shi da yake da shi ga mutanen kasuwar.

No comments