Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Karamar Hukumar Dandume Ta Yi Sabon Shugaba

  Daga Hussaini Yero Sakamakon gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Radda da ya ba shugaban karamar hukumar Dandume Hon. Ya'u Nowa, mukamin ...

 

Daga Hussaini Yero

Sakamakon gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Radda da ya ba shugaban karamar hukumar Dandume Hon. Ya'u Nowa, mukamin mai bashi shawara akan ayyukan da karin girma doka ta tabbatar da mataimakinsa ya maye gurbin shugaban karamar hukumar ta Dandume.

Mataimakin shugaban karamar hukumar, Basiru Musa Dandume ne ya zamo shugaban karamar hukumar Dandume a yanzu haka, sai kuma Hon. Abdullahi Takalmawa ya zama mataimakin Shugaban Karamar hukumar.

Mai Sharia a  Kotun Majistiri da ke Funtua ne Samsudini Abdullah ya rantsar da su kamar yadda doka ta tanada.

A jawabinsa Shugaban mulki da kudi na karamar hukumar Dandume, Alhaji Nura Suleman 'Yan Daki ya yi kira ga ma'aikatan Karamar hukumar Dandume da su ba sabon Shugaban karamar hukumar goyan baya domin samun nasarar ayyukan ci gaba da karamar hukumar ke kan yi a yanzu haka.

Babban bako a wajen rantsarwar shi ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Katsina, Ado Ladan, ya yi kira ga sabon shugaban karamar da ya yi aiki tsakanin da Allah kuma ya kula da mutane ba tare da bambancin siyasa ba dan samun nasarar ayyukansa.

No comments